Nigeria: Tarin shika 'ya hallaka' yara 11 a Kano

Ana danganta annobar tarin shika ne da rashin yin alluran riga-kafi akai-akai da kuma rashin ingantaccen tsarin lafiya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana danganta annobar tarin shika ne da rashin yin alluran riga-kafi akai-akai da kuma rashin ingantaccen tsarin lafiya

Rahotanni daga karamar hukumar Kiru ta jihar Kano a Najeriya na cewa cutar tarin shika, ko (kwato-kwato) ya yi sanadiyyar mutuwar kananan yara 11, yayin da ake ci gaba da bai wa wasu kimanin 40 magani bayan da suka kamu da ita.

Tun da fari dai jami'in yada labarai na yankin ne Rabi'u Khalil ya fitar da sanarwar.

Sai dai kwamishinan lafiya a jihar ta Kano, Dr Kabir Ibrahim Getso, wanda shi ma ya tabbatar wa BBC bullar cutar a karamar hukumar ta Kiru da wasu yankunan jihar, ya musanta rahotannin cewa an samu hasarar rayuka.

Hukumomi dai sun ce suna bakin kokarinsu don shawo kan annobar kafin ta munana.

Ana danganta annobar tarin shika ne da rashin yin alluran riga-kafi akai-akai da kuma rashin ingantaccen tsarin lafiya.

Mene ne tarin shika?

Cutar ta tarin shika dai ta fi kama kananan yara da jarirai, inda sukan yi ta tari da kuma fuskantar wahalar numfashi, kuma tana saurin halaka su.

Wasu kwayoyin cuta da ake kira Bordetella pertussis ne ke jawo tarin shika.

Alamun farko-farko na cutar su ne mura, sai kuma tari mai tsanani

Kalar jikin yara kan sauya zuwa shudi idan suna tarin saboda karancin iskar shaka

Tarin kan zo akai-akai kuma idan ana yi yana sarke mutane

Manyan ma na iya kamuwa da cutar

An gargadi 'yan Nigeria kan zuwa asibitocin kasashen waje

Yaushe Buhari zai soma yi wa jama'ar Kano aiki?

Mutum uku ne suka kamu da cutar kyandar biri a Nigeria - WHO

Labarai masu alaka