Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu zababbun hotunan al'amuran da suka faru a Afirka da kewaye, a makon nan.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Sandra Kouadio ta yi kitson zamani da ake ya yi a babban birni Ivory Coast, Abidjan.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Simon Nkendoh yana jiran masu zuwa aski a cikin shagonsa.

Hakkin mallakar hoto AFP

Masu tallan kayan kawa na yin shirin makon nuna kayan ado na Kinshasa a babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wata mai yin kwalliya ke nan take amfani da fitilar wayarta ta hannu a lokacin da take yi wa wata kwalliya

Hakkin mallakar hoto JOHN WESSELS

Wata mai tallan kayan kawa tana nuna ado irin na Congo

Hakkin mallakar hoto EPA

A ranar Laraba ne wasu 'yan Morocco suke sukuwa da dawakai birnin el-Jadida da ke kudancin Casablanca.

Hakkin mallakar hoto EPA

Wasu masu sukuwa da dawakai dauke da wata tuta mai cin wuta .

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Alhamis ne wasu masu rawa suke kwalliya kafin su fara rawa a bikin Diwali, a kudancin Afirka.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Talata ne wadanann masu rawa suke rakashewa a taron matan shugabannin Afirka a kan yaki da bautar da yara.

Hakkin mallakar hoto EPA

Wasu yara ke nan da suka daura wata takarda a kansu da ke hana nuna bambanci tsakanin maza da mata a babban birnin Laberiya, Monrovia.

Hakkin mallakar hoto EPA

Mutanen da ba su da halin sayen jarida ko sayen data suyi amfani da wayarsu ta hannu don ganin yadda ake gudana a zaben shugaban kasar Laberiya, na zuwa inda ake rubutu a wani allo babbar hanyar birnin garin don ganin halin da ake ciki.

Hakkin mallakar hoto EPA

A ranar Litinin ne wasu mutane suke zagayawa a kusa da wata kwantena da aka yi a gundumar Mabonengt da ke Johannesburg babban birnin Afirka ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto EPA

Wani yankin karkara ya zama birni, bayan da jami'an birnin suka kaddamar da wani shiri na bunkasashi.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Asabar ne dan kwallon Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ke yin murna bayan da suka samu nasara.

Labarai masu alaka

Labaran BBC