Wazirin Sarkin Musulmin Nigeria Alhaji Usman Junaidu, ya rasu

Wazirin Sokoto Hakkin mallakar hoto Waziri's family
Image caption Wazirin Sokoto

Allah ya yi wa Wazirin Sarkin Musulmin Sokoto Alhaji Usman Junaidu rasuwa ranar Juma'a da safe.

Marigayi Usman Junaidu dai ya rasu yana da kimanin shekaru 90 a duniya.

Ya rasu ne bayan ya yi fama da doguwar jinya a Sakkwaton.

Waziri Usman dai shi ne na 12 a jerin Waziran Sarkin Musulmi da aka yi a tsawon shekara 200 na daular Usmaniyya.

Tuni aka yi jana'izar marigayin a birnin Sakkwato.

Ya rike mukamin wazircin Sokkwato na tsawon shekara 20.

Shi ne na biyu a majalisar masarutar Sarkin Musulmi ta Sokoto bayan sarkin Musulmin kansa.

Labarai masu alaka