IS ta ce ita ce ta kashe 'yan Shi'a 40 a masallaci

Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters

Kungiyar ISIS ta ce ita ce ke da alhakin harin da aka kai kan masallacin 'yan Shi'a ranar Juma'a a Kabul babban birnin Afghanistan, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 40.

Ta ce daya daga cikin 'yan kunar-bakin-wakenta ne ya fara harbi da bindiga kan masu ibada kafin ya ja kunamar bama-baman da ya yi jigida da su.

Akalla mutum 60 ne aka kashe a hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan masallatai guda biyu a kasar ta Afghanistan, kamar yadda jami'an kasar suka bayyana.

Harin da aka kai masallacin Shi'a ya kashe kusan mutum 40 ciki har da mata da kananan yara.

Akalla mutum 20 kuma sun mutu yayin da wani maharin ya tayar da bam a wani masallacin Sunni da ke gundumar Ghor.

Karanta wadansu karin labarai

Kungiyar ISIS ba ta ambaci hari na biyu da aka kai kan masallacin 'yan Sunni a tsakiyar lardin Ghor, inda mutum 20 suka halaka ba.

Daga cikin wadanda aka kashe har da kwamandan sojojin sa-kai masu goyon bayan gwamnati.

Haka zalika da sanyin safiyar Asabar kuma rokoki sun fashe a yankin Green Zone mai matukar tsaro a Kabul, ko da yake, babu rahotanni mutuwa ko jikkata.

Labarai masu alaka