An kashe 'yan sandan Masar 53 a kwanton bauna

Egypt attack Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan ta-da-kayar-baya sun sha far wa dakarun tsaron Masar da kuma fararen hula masu ibada a mujami'u

Gwamnatin Masar ta ce wani artabu tsakanin jami'an tsaronta da wasu 'yan ta-da-kayar-baya ya yi sanadin mutuwar akalla 'yan sanda 53 a yankin Saharar Kudancin kasar.

Haka zalika, an kashe su ma 'yan ta-da-kayar-baya 15.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce 'yan ta-da-kayar-baya sun bude wuta kan jami'an tsaron ne lokacin da suka kai wa maboyarsu samame a kusa da dausayin Bahariya.

Masar na fama da ayyukan 'yan ta-da-kayar-baya da ke tattare a yankin Sinai, akasari daga wasu manyan kungiyoyi guda masu alaka da ISIS.

Hare-haren 'yan ta-da-kayar-bayan dai ya yi sanadin mutuwar dakarun tsaron kasar da dama tun cikin shekara ta 2013.

Rahotanni sun ce an yi wa jami'an tsaro kwanton bauna ne, inda 'yan tada-kayar-baya suka far wa motocinsu da bindigogin roka.

Wata majiyar tsaro ta ce 'yan ta-da-kayar-bayan sun fi sanin yankin ciki da bai, kuma kwamandan jami'an tsaron ya gaza kiran a kai masa dauki.

Wani rahoto ya ce 'yan ta-da-kayar-bayan sun fito ne daga wata kungiya da ake kira Hasm, wadda ta saba far wa dakarun tsaro a baya.

Labarai masu alaka