An yi tir da ba Robert Mugabe mukamin farin jakada

Mutane na mamaki kan mukanin farin jakada da aka yi wa Mugabe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane na mamaki kan mukanin farin jakada da aka yi wa Mugabe

Kungiyoyin kare hakkin dan'adam da jam'iyyar adawa a Zimbabwe sun yi tir da shawarar Hukumar Lafiya a Duniya ta nada Shugaba Robert Mugabe matsayin farin jakada

Kungiyar Human Rights Watch ta ce la'akari da tarihin Mugabe kan batun 'yancin bil'adama, abin kunya ne ba shi irin wannan mukami.

Jam'iyyar adawa a Zimbabwe ta ce matakin abin dariya ne don kuwa a kan idon Mugabe ne tsarin kula da lafiyar kasar ya rushe. Hukumar lafiya ta duniya ta nada shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, a matsayin farin jakada.

Sabon babban daraktan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ne ya sanar da nadin a wajen wani taro da aka yi a kan cutukan da ba sa yaduwa a Uruguay.

Nadin shugaban kasar ta Zimbabwe mai kimanin shekarA 93 ya haifar da ka-ce-na-ce a tsakanin kasashe mambobin hukumar da ma kungiyoyin agaji.

Farin jakada, mukami ne na mutumin da ya taka wata muhimmiyar rawa, to amma ba da shi ga mutumin da ake sukar gwamnatinsa a kan rugujewar tsarin kula da lafiya da kuma gagarumin cin zarafin bil'adama, ba abu ne mai karfafa gwiwa ba.

Sabon babban daraktan ya yaba wa shugaban na Zimbabwe bisa kokarinsa wajen kula da lafiyar al'umma, wanda a cewarsa hakan ne ya sa ba shi wannan matsayi.

An ba Robert Mugabe mukamin ne don ya taimaka wa hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya shawo kan cutukan da ba a yada su.

Dr Tedros, shi ne dan Afrika na farko da ya taba rike wannan babban matsayi, kuma an zabe shi ne bisa alkawarin kawo sauyi a hukumar da kuma shawo kan yadda wasu ke jin ana sanya siyasa cikin al'amuran hukumar.

Mataki na sabon daraktan zai sanya shakku a zukatan wasu game da yanayin shugabancinsa da ma ayyukansa.

Labarai masu alaka