Ana sake tunani a kan farin jakada Mugabe

Mutane na mamaki kan mukanin farin jakada da aka yi wa Mugabe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane na mamaki kan mukanin farin jakada da aka yi wa Mugabe

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana sake nazari kan shawarar nada shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a matsayin farin jakadanta.

Bayan fuskantar suka daga fadin duniya, sabon shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce nan gaba kadan zai fitar da wata sabuwar sanarwa.

Burtaniya da Amurka sun bayyana takaicinsu a bainar jama'a game da wannan nadi.

Yayin da 'yan adawan kasar suka ce Hukumar Lafiya ta Duniya, raha ce kawai take yi.

Sai dai magoya bayan Mugabe sun bayyana nadin a matsayin karramawa da ta dace ga dattijon Afirka.

Masu sukar lamiri sun ce a hannunsa tsarin kula da lafiyar Zimbabwe ya rushe, yayin da tattalin arzikinta ya tabarbare.

Kungiyoyin kare hakkin dan'adam da jam'iyyar adawa a Zimbabwe sun yi tir da shawarar Hukumar Lafiya a Duniya ta nada Shugaba Robert Mugabe matsayin farin jakada

Kungiyar Human Rights Watch ta ce la'akari da tarihin Mugabe kan batun 'yancin bil'adama, abin kunya ne ba shi irin wannan mukami.

Jam'iyyar adawa a Zimbabwe ta ce matakin abin dariya ne don kuwa a kan idon Mugabe ne tsarin kula da lafiyar kasar ya rushe.

Labarai masu alaka