'Yan gudun hijra na karo-karo don ba 'ya'yansu ilimi

Yara na karatu a sansanin 'yan gudun hijra Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara na karatu a sansanin 'yan gudun hijra

Halin tagayyara da dugunzumar da rikicin 'yan ta-da-kayar-baya na Boko Haram ya jefa wasu 'yan gudun hijira, ba su sanyaya musu gwiwar ilmantar da 'ya'yansu ba a sansanonin da suke samun mafaka.

'Yan gudun hijirar sun tashi tsaye don nema wa 'ya'yansu mafita ta hanyar kafa makarantar Islamiyya da taimakon kungiyar Women In Da'awa.

Wakiliyar BBC Badriyya Tijjani Kalarawi, ta ziyarci Tudun Mun Tsira, wani sansanin 'yan gudun hijira da ba na gwamnati ba da ke unguwar Karmo a Abuja babban birnin Najeriya, inda ta ga yara na karatun islamiyya a wani waje da aka kewaye da langa-langa.

Malama Hassana Abdullahi, na daya daga cikin malaman da ke koyarwa a wannan islamiyya, ta kuma ce ita ma a sansanin take da zama.

Malamar ta ce da su uku ne ke koyarwa a makarantar amma sai iyayen yaran da ke zaune a sansanin suka lura cewa malaman sun yi kadan, don haka suka yanke shawarar karo wasu, idan ya so sai su rika karo-karo suna biyansu albashi a duk wata.

Hassana Abdullahi ta ce, wannan shawara da iyayen yaran suka yanke, ta yi matukar tasiri wajen samar da ilimi ga yaran da ke zaune a sansanin na Tudun Mun Tsira kasancewar ba ya karkashin kulawar gwamnati.

Labarai masu alaka