Adikon
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Tazarar haihuwa na rage mace-macen mata'

  • Akwai tattaunawar da Fatima Zahra Umar ta yi da wadansu mata da kuma likita game da wannan batu, za ku iya saurara idan kuka latsa alamar lasifika da ke sama.

A lokuta da dama idan mutum ya ji ana maganar batun hana daukar ciki ko kuma tsarin iyali, a kan danganta abin ne kawai da halaccinsa ko kuma akasin hakan.

Da wuya ka kaji matar aure tana ba da labarin hanyoyin da take bi wajen kaucewa daukar juna biyu.

Ko mene ne yake hana su yin hakan?

Yana da muhimmanci matuka idan mata za su ba da labarin abin da suka fahimta game da amfani da dabarun tsarin iyali.

Don haka a wannan makon filin Adikon Zamani zai tattauna ne da matan da suka zabi amfani da tsarin iyali.

Wadansu daga cikin matsalolin amfani da magungunan tsarin iyali da ta fi damun mata su ne: matsalolin al'ada, hararwa, ciwon mama, ciwon kai, teba, rage musu sha'awa, fitowar wani ruwa daga al'aurarsu da kuma tsalalolin gani.

Girman irin wadannan matsalolin ya danganta ne daga mace zuwa mace.

Kuma akan daina ganinsu bayan wasu makonni da fara amfani da magungunan tsarin iyali.

Malama Fatima wadda take da 'ya'ya uku, ta kwashe kimanin shekara bakwai tana amfani da magungunan tsarin iyali.

Kuma a cikin wadannan shekaru bakwai din ne ma ta taba samun haihuwa.

Hakan nuna cewa ba gaskiya ba ne batun da ake yi cewa amfani da magungunan tsarin iyali yana dakatar da haihuwa gaba daya.

Ta ce tana iya daukar ciki duk lokacin da ta so.

Abin da kawai za ta yi shi ne ta daina amfani da magungunan tsarin iyali.

Likitoci suna ba mata shawara kan amfani da tsarin iyali saboda muhimmancin daidaita adadin 'ya'ya da kuma samun iyali.

Kamar yadda likitoci suka ce idan mace ta haihu jikinta na bukatar hutu kafin ta kara daukar wani sabon cikin.

Jikin mace yana bukatar hutun akalla shekara biyu kafin ya sake goyon wani cikin, a cewar Dokta Habiba Ibrahim.

Samun wani cikin kafin cika shekara biyu zai iya jawo barazana ga lafiyar mace.

"Juna biyu tana tattare da manyan kalubale ga uwa da kuma jaririn da ke cikinta don haihuwa wata nauyi ce ga uwa saboda haka yana da kyau a bar jikin mace ya dan huta kafin sake daukar wani cikin," in ji Dokta Habiba.

Amfanin tsarin iyali fili yake kuma abu da kowa zai iya gani a zahiri.

Za ku iya bayyana ra'ayoyinku game da wannan batu a shafukannu na Facebook, Twitter da kuma Instagram.

Labarai masu alaka