Hukumar WHO ta soke mukamin da ta ba Robert Mugabe

Mugabe Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta soke sabon mukamin farin jakada da ta bai wa Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe bayan ta sha matsin lamba.

"Na saurari duka korafe-korafen da jama'a suka yi cikin nutsuwa," in ji sabon Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus a wata sanarwa da ya fitar.

Sai dai shugaban ya taba yaba wa Zimbabwe game da yadda take aiki tukuru a fannin kiwon lafiyar al'umma.

Sai dai wadansu masu sharhi suna ganin fannin kiwon lafiyar kasar ya tabarbare karkashin mulkin shekara 30 na Mugabe.

A ranar Juma'a ne hukumar ta nada shugaban matsayin farin jakadanta, abin da ya jawo kakkausar suka daga kungiyoyi da mutane dama a duniya.

Labarai masu alaka