"Dole Buhari ya kama AbdulRasheed Maina"

FACEBOOK/ABDULRASHEED MAINA Hakkin mallakar hoto AFP

Masu fafutuka a Najeriya sun ce ya zama wajibi Shugaban Muhammadu Buhari ya kama tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar AbdulRasheed Maina, in har da gaske yake yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban kwamitin da ke bai wa Shugaba Buhari shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, yana sahun gaban cikin masu kira ga shugaban Najeriyar ya sa a kama tare da hukunta AbdulRasheed Maina.

Farfesa Sagay ya ce ya kamata a hukunta duk wanda yake da hannu a mayar da AbdulRasheed Maina bakin aiki domin su ma sun taimaka wajen aikata laifi.

Baya ga Farfesa Itsey Sagay, fitaccen lauyan nan, Femi Falana, shi ma ya fito ya ce dole a kama AbdulRasheed Maina domin ya amsa tuhume-tuhumen da hukumar EFCC take masa.

Ya kuma ce ya zama wajibi a hukunta dukkan masu hannu a mayar da Maina aiki domin suna neman su hana ruwa gudu ne a yakin da shugaban kasar ke yi da cin hanci da rashawa.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce: "Ana mayar da wanda ake tuhuma da satar biliyoyin nairori bakin aiki, kuma kuna tunanin Buhari yana yaki da cin hanci da rashawa."

Wasu da aka sani da goyon bayan gwamnatin Shugaba Buhari da ke da mabiya a shafukan sada zumunta irin su Omojuwa ma, sun yi tir da mayar da Abdulrasheed Maina bakin aiki.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Omojuwa ya ce wannan abin kunya ne ga gwamnatin Shugaba Buhari.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta fara neman Abdulrasheed Maina ruwa-a-jallo ne a shekarar 2015 kan zargin yin sama da fadi da naira bliyan biyu cikin kudin yin garam bawul wa tsarin fanshon Najeriya.

A wancan lokacin har zanga-zanga wasu suka yi zuwa majalisar dokokin Najeriya domin nuna goyona baya ga Abdulrasheed Maina.

Amma bai fito ya kalubalanci neman da ake yi masa ba.

Bayan EFCC ta yi shelar nemansa ne aka daina jin duriyar Maina.

Ba a sake jin labarinsa ba sai lokacin da rahotanni suka ce ya koma aiki a ma'aikatar cikin gida ta Najeriya, a matsayin daraktan riko.

Amman ministan ma'aikatar cikin gidan, Abdulrahman Dambazau, ya ce shi bai san komai ba dangane da dawowar AbdulRasheed Maina aiki.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran ministan, Ehisienmen Osaigbovo, ya fitar ta ce daga ofishin shugaban ma'aikatan Najeriya ne aka turo Abdulrasheed aiki a ma'aikatar.

Saboda haka ministan bai san yaya aka yi Abdulrasheed Maina ya dawo ma'aikatarsa ba.

Mai magana yawun hukumar EFCC ya tabbatar da cewa, har yanzu hukumar tana neman AbdulRasheed Maina, ruwa-a-jallo.

Bugu da kari, sanarwar da hukumar EFCC ta bayar cewar tana neman Maina har yanzu tana nan a shafinta na Intanet.

Image caption Har yanzu dai hukumar EFCC dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta ce tana neman AbdulRasheed Maina ruwa-a-jallo

Labarai masu alaka