'Yan BH na jin takaicin ana cewa suna lalata da mu - 'Yar Chibok

Naomi Adamu

Daya daga cikin 'yan matan Chibok da aka sako a watan Mayu ta shaida wa 'yar jarida Adaobi Tricia Nwaubani yadda ba za ta manta da abubuwan da suka faru da ita a cikin shekara uku da ta shafe a hannun mayakan Boko Haram ba.

Naomi Adamu na daya daga cikin wadanda suka fi yawan shekaru a ajinsu kuma tana da shekara 24 a lokacin da 'yan Boko Haram suka sace su, suka boye su a dajin Sambisa da ke arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2014.

A lokacin da suke hannun mayakan, sun ba su littattafan rubutu da suke zuwa da su aji a lokacin da suke koyon karatun Kur'ani.

Sai dai wasu daga cikin yaran na amfani da wadannan littattafan rubutu ne wajen rubuta abin da ya faru da kuma sirrikansu. A lokacin da mayakan suka gano haka ne suka tilasta musu kona littattafan.

Sai dai Naomi da kawarta wacce ko da yaushe suna tare wato Sarah Samuel, mai shekara 20 sun yi kokarin boye nasu littafin, da wasu 'yan mata uku wadanda su ma suka yi amfani da littatfin wajen adana labarinsu da kuma halin da suka shiga.

Bayanan hoto,

Littattafan biyu ne masu shafi 40 wadanda 'yan matan suka adana don rubuta labarin halin da suka shiga

An yi rubutun cikin littafin ne a harshen Turanci da kuma Hausar da ba ta nuna, sai dai ba a rubuta kwanan wata a jiki ba, amma ana ganin an yi rubutun ne tun a watannin farko na kama 'yan matan.

Ga goma daga cikin abubuwan da suka rubuta. Sai dai an dan yi gyare-gyare a wasu wuraren don a fahimta sosai:

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

1. Ba da niyyar sace 'yan matan Chibok aka je ba

Mayakan da suka kai hari makarantar Chibok a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, sun je da niyyar sace "injin da ake buga bulo ne" kamar yadda 'yan matan suka rubuta a littafin.

Sai dai ba a san takamaimai injin da suke nema ba, saboda an yi aikin gine-gine a makarantar na wasu 'yan makonni, amma wata kila injin da ake yin bulon siminti suke nema wanda kuma ana amfani da shi a wajen kera makamai.

Sai dai da ba su samu ba ne, sai suka fara shawarar ya za su yi da daliban da suka taru kungiya-kungiya. Bayan da suka dauki lokaci suna wannan mahawara ne sai suka yanke shawarar tafiya da yaran.

"Sun fara mahawarar ne a tsakaninsu. Sai wani karami daga cikinsu ya ce a kona mu duka kawai, sai suka ce a'a ba haka za a yi ba, mu tafi da su dajin Sambisa.

"Sai wani kuma ya ce, 'a'a kar mu yi haka, mu kai su gidan iyayensu. Suna cikin wannan mahawarar ne sai daya daga cikinsu ya ce, gaskiya ba zai yiwu na zo da mota ba komai cikinta sannan kuma na koma da ita fanko ba, idan muka kai su wajen shugabanmu (Abubakar Shekau) zai san yadda za a yi."

2. Labarin yadda aka kange su daga tserewa

An zuba wasu daga cikin yaran cikin motar da mayakan suka zo da ita makarantar, da dama kuma aka sa su suka fara tattaki da kafarsu ana binsu da bindigogi inda suka yi doguwar tafiya, har sai da aka kawo wasu motocin da suka dauki sauran 'yan matan.

Wa ya rubuta labarin?

Ainihin wadanda suka rubutawa: Naomi Adamu da Sarah Samuel

Rhoda Peter da Saratu Ayuba da Margaret Yama sun ba da 'yar gudunmowa wajen rubutun

An sako hudu daga cikinsu a watan Mayun 2017

Sarah Samuel ta yarda ta auri daya daga cikin mayakan a bara kuma har yanzu tana wajen su.

Bayanan hoto,

Wannan shi ne littafin da Naomi ta dinga rubuta abin da ke faruwa

A kan hanyarsu ta zuwa dajin da aka boyesu, sai wasu daga cikin daliban suka fara tsalle suna dira daga motar suna tserewa, amma sai daya daga cikin su ta sanarwa da mayakan.

Wata kila ta yi hakan ne don tana jin tsoron kar a tafi a bar ta ita kadai, ko kuma don yin biyayya ga dokar da aka ba su.

"Sai daya daga cikin 'yan matan ta ce, 'Direba wasu yaran suna tsalle suna tserewa. Sai direban ya bude kofar motar ya fara nemansu amma bai samu ko daya ba. Sai suka ce musu su zauna wuri daya, kuma idan suka samu wata ta kara tsalle ta fita sai sun harbeta."

3.Mugayen dabaru

Mayakan sun yi amfani da mugayen dabaru a kan 'yan matan da suka sace, da suka hada da barazanar cewa tuni mayakan suka sace iyayensu.

A wani lokacin kuma suna ware Kirista dabam Musulmai dabam, har ma su ce duk wanda bai Musulunta ba za su konashi da fetir.

"Sanann sai suka zo wurinmu suka ce mana, Musulmai su fito lokacin sallah ya yi. Bayan da suka idar da sallah sai suka ce, Musulmai su ware Kirista ma su ware gefe daya".

"Sai muka ga wasu jarkoki a mota sai muka yi tsammanin fetir ne. Sai suka ce mana, Su waye zasu Musulunta a cikinku. Da yawa daga cikinmu suka tashi tsaye suka shiga ciki saboda tsoro, sai suka ce, ku sauran kuna so ku mutu kenan tunda ba kwa son ku Musulunta ko?

"To zamu kona ku, sai suka ba mu wadanann jarkokin da muka yi tsammanin fetir ne ashe ruwa ne a ciki."

4. Mayakan na jin takaci a kan zargin da ake yi a kansu cewa suna lalata da 'yan matan

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka tattauna da su sun bayyana cewa ba a yi lalata da su ko tilasta musu aure ba, ko da yake wani lokacin sun nuna bukatar aurensu.

Wasu 'yan matan kuma ana daukarsu a matsayin kwarkwara.

Bayanan hoto,

'Yan matan sun boye litatfin da suka yi rubutun a karkashin kasa

Rubutun ya nuna cewa mayakan suna jin haushin abin da kafafen yada labarai ke yada wa cewa suna lalata da 'yan matan.

Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya sha fadar haka a lokuta da dama, na farko a wani sakon da aka nada da aka kunana wa 'yan matan.

"Sannan da dare kuma, suna taramu suyi mana wa'azi kuma su kunna mana kaset.

"Sun ce kaset din daga wurin shugabansu yake Abubakar Shekau, inda ya ce ba don wani abu aka daukoku ba sai don a koya musu addini da bin hanyar Allah, amma iyayenku da gwamnati da shugaban makarantarku suna yin kuka suna cewa muna yin lalata da ku, muna yi muku abubuwa marasa kyau, to mu mun kawoku ne don mu koyar da ku hanyar Allah."

5. Saka hijabi don gujewa rudin shedan

Mayakan na fadakar da 'yan matan muhimmancin saka hijabi a ko yaushe don kar su jefa su a rudin shaidan su yi sha'awar jikinsu.

Asalin hoton, AFP/Boko Haram

"Ya bude Kur'ani ya fara karantawa, sannan ya karanta wani wuri da ya fassara da cewa duk wanda aka sace a jihadi, to naku ne kuma kana da damar da zaku yi abin da ku ke so da shi, saboda haka ne sai suka ba mu hijabi saboda ba sa so suna ganin jikinmu, saboda kar su aikata sabo kuma su yi abin da bai dace ba".

6. Gabatar musu da bukatarsu ta neman aure

Mayakan boko haram suna yawan tilasta wa 'yan matan da maganar aure.

"Wata yarinya tana so ta shiga daki ta dauki wani abu, sai wani daga cikin mayakan (Malam Ahmad) ya shiga ya sameta ya yi mata magana a kan aure. Sai ta ce masa, a'a, sai ya tambayeta, mece ce shawararki game da auren?

"Sai ta ce a'a, sun sato ta daga makarantar GGSS Chibok sun kawota Sambisa sannan kuma yanzu suyi mata maganar aure.Ta yaya za ta yi aure bayan mahaifiyarta da mahaifinta da sauran 'yan uwanta ba su sani ba.

"Sannan sai ta tambayeshi idan ta ce a'a ba za ta yi auren ba, kawai za ta tsaya ta yi wa ubangijinta biyayya kawai, ta yi laifi? sai ya ce a'a, ba laifi".

Wasu kuwa an matsa musu lamba don su sauya ra'ayinsu.

"Mun ga mutane suna fitowa daga mota kirar (Hilux). Sai suka tambayemu su waye suke son yin aure. Kuma suka ce mana duk wanda ya Musulunta to dole ne ya yi aure matukar ya rungumi addinin hannu bibbiyu.

Sai suka ba mu minti 30 mu ba su amsa amma sai muka yi shiru. Mun shafe sa'a daya ba wanda ya ce musu uffan".

Naomi Adamu ta shaida min cewa duk wadanda suka ki amincewa su yi aure ana daukarsu a matsayin bayi, kullum sai an dake su.

Suna fada mana cewa mu yi aure idan ba haka ba za su dakemu. Mu yi wanki, mu debo ruwa, mu zamu yi wa matansu komai, mu kuma bayi ne".

7. Mazauna wani kauye sun dawo da wadanda suka tsere

Duk da fafatukar da aka yi ta yi a duniya don ganin an dawo da yaran nan, inda har shahararrun mutane da dama a duniya suka tsoma baki, wasu mutanen kuwa ba sa so su zama wani bangare na wannan fafutuka don da suka tsinci 'yan matan da suka yi koarin tserewa sai suka dawo da su hannun mayakan.

Asalin hoton, AFP

"Akwai wata rana da wasu yaran suka gudu. Suna kokarin su tsere amma sun kasa. Sai wadanan mutane suka kamasu. Yadda aka yi suka kama su kuwa shi ne, sun shiga wani shago suka ce a taimaka musu a basu ruwa da biskit.

"Sai mutanen suka tambayesu, su waye ku kuma daga ina kuke? Sai yaran suka ce, mu ne wadanda kungiyar Boko Haram ta sace daga GGSS Chibok. Sai daya daga cikin mutanen suka ce ku ba 'ya'yan Shekau ba ne?"

"Sai suka ba su abinci mai kyau suka ci suka ba su wurin kwana, washe gari kuma suka dawo da su wurinmu, ... Bayan sun dawo da su dajin Sambisa da daddare, sai aka zane su kuma zasu kaisu a yanke musu wuya."

8. Tilastawa a kan su Musulunta

An shaida wa 'yan matan cewa za a bar su su koma gida wurin iyayensu ne kawai idan dukkansu suka amince za su Musulunta. Wadanda ba su amince ba kuma za su ci gaba da rikesu.

"Sai suka ce wadanda ba su musulunta ba tamkar tumaki da shanu da akuyoyi ne .... za su kashe su...

"Sai daya daga cikinsu da ake kira, Malam Abba ya ce duk wadanda ba su musulunta ba su ware gefe daya kar su shiga cikin wadanda suka musulunta. Sai ya ce mu tsaya gefe daya, don za su ware musu wani wuri dabam.

"Sai wani mutumin daban yace a'a mu tsaya waje daya. Bayan an yi haka da mako guda, sai sauran 'yan uwanmu suka ce mu da muka ki zama musulmai, mu ke jawo manat tsaiko wajen komawarmu gida wajen iyayenmu."

9. Yadda ake daukar bidiyo

Boko haram ta saki bidiyo da dama game da 'yan matan Chibok. Ga yadda suke shirya daya daga cikin bidiyon:

Asalin hoton, AFP/Boko Haram

Bayanan hoto,

We have blurred the girls' faces as some former Boko Haram captives and "wives" have been stigmatised after their release

"Sannan kuma akwai wata rana kafin nan, da suka zo suka dauki bidiyon kusan 'yan mata10 da suka tara su a karkashin bishiyar tsamiya.

"Suna kiransu daya bayan daya suna tambayarsu sunansu da sunan iyayensu, sannan sai suka ce juyo wurinmu suka ce, 'Mun taba cutar da ku? Muka ce a'a. Sai suka ce mana mu fada wa iyayenmu da gwamnati abin da suke mana. Gwamnati da iyayenmu suna cewa suna lalata da mu da kuma gallaza mana".

"Sai suka kira daya daga cikinmu suka tambayeta, tun daga lokacin da muka daukoku wannan wurin kin taba kwana da wani ko an yi lalata da ke?

"Sai ta ce a'a, suka kara ce mata, ina so ki nunawa iyayenki da gwamnati abin da muke muku da kuma yadda muke kula da ku".

10. Mayakan Boko Haram na sauraran labarai sosai

Wani lokaci ana shirya bidiyon ne da zarar mayakan sun gama sauraron labarai.

"Akwai lokacin da bayan sun gama sauraron BBC Hausa, sai suka kira mu daya bayan daya. Sai suka ce wasu su tsaya wasu su durkusa wasu kuma su zauna, sauka dauki bidiyonmu muna karatun Kur'ani."

Me ya faru da wadanda suka rubuta labarin?

Naomi Adamu da wasu mutum uku da suka rubuta labarin da suka hada da Rhoda Peter, da Saratu Ayuba da kuma Margaret Yama duk an sako a watan Mayu.

A watan Satumba ne, gwamnati ta tura su karatu jami'ar Amurka ta Yola a arewa maso gabashin Najeriya.

Naomi Adamu wacce ita ce ta biyu a gidansu ta ce, ta adana labarin da ta rubuta a lokacin da take cike da kawa-zucin iyayenta.

"Na rubuta abubuwan da suka farun ne don ya zama tarihi," in ji ta.

"Don 'yan uwana da iyayena su gani."

Bayanan hoto,

Mahaifiyar Naomi Adamu ba ta iya karatu ba amma ta kagu ta san abin da rubutun ya kunsa

Mahaifinta Samuel Yaga ya shaida min cewa bai yi mamaki yadda aka yi 'yarsa ta yi rubutun a lokacin da suke tsare ba.

"Ko da yaushe a cikin karatu take. Wani lokacin ma littafinta yana kan cinyarta bacci zai dauketa," in ji shi.

A shafin karshe na littafin ne ta rubuta sunan kannenta biyar, ta kuma rubuta sunan mahaifinta Samuel da mahaifiyarta Rebecca.