'Yadda mijina ya ke karfafa min gwiwar yin sana'a'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon hira da Rukayya mai sana'ar mai

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon hira da Rukayya Igabi:

Rukayya AbdulWahab Igabi, wata mata ce mai yin man shafawa da man kitso da shamfo da sabulun wanke-wanke har da ma turare na jiki a birnin Kano.

Ta shaida wa BBC cewa ta fara wannan sana'ar ce bayan da mijinta ya halarci wani taro shekara 17 da suka gabata, inda aka bashi kyautar wani littafi wanda a cikinsa ne aka yi bayanin yadda ake sarrafa wadannan abubuwa.

Ta ce daga farko, da ta koyi yadda ake hada mayukan da turarukan, ta kan yi ne domin ta yi wa 'yan uwanta kyauta ko kuma ta yi tsaraba idan za ta ganin gida.

Ta yanke shawarar fara sarrafa kayan don ta sayar ne bayan da ta fuskanci cewa mutane na yawan tambayarta a kan yadda za su samu kayan.

Kalubale

Rukayya ta ce akwai wasu 'yan matsaloli da ta fuskanta a fannin wannan sana'ar kamar hauhawar farashin sinadaren da ta ke amfani da su wanda ya jawo ko dai a rasa riba ko kuma a tsira da uwar kudin da kyar.

Wata matsalar kuma ita ce ba ta da waje na musamman da za ta iya aikinta hankali kwance, tun da aikin hada wadannan mayuka da sabulai aiki ne mai hadari ganin cewa sai an tafasa sinadaran kuma tana da yara kanana.

Ta ce don haka sau da yawa sai tsakar dare ta ke iya yin aikin hada sabulan da mayukan domin a lokacin yaranta sun yi bacci.

Wata matsalar da Ruqayya ta ce tana fuskanta kuma shi ne na rashin na'urar tuka sabulun a yayin da ake hada shi.

Image caption Rukayyar ta ce daga farko, da ta koyi yadda ake hada mayukan da turarukan, ta kan yi ne domin ta yi wa 'yan uwanta kyauta

Ta ce sau da yawa sai an taya ta tukawa inda maigidanta ma ya kan taimaka mata da tukin.

Nasarori

Rukayya ta ce ta samu nasarori da dama dalilin wannan sana'a don kuwa ta ce ta na biyan bukatunta da na yaranta har ma da na 'yan uwanta.

Kuma a kan kira ta a waya a bukaci da ta aika sabulan ko mayukan jihohi daban-daban na Najeriya.

"Yarana sun bude min shafin sada zumunta na Facebook inda a nan ma suna tallata min kayana kuma ina samun kasuwa sosai.

"Wasu kuma su kan bukaci na koya musu yadda ake hada wadannan kayayyakin, kuma ba na karbar kudi a hannunsu wai don ta koya musu sana'ar.

"Hasali ma, wasu a waya su ke kirana na yi musu bayanin yadda za su hada kayan a gidajensu. "

Ta ce babban burin da ta ke da shi a sana'arta, shi ne ta samu wajen aiki nata na kanta.

Ta kuma ce maigidanta shi ne kashin bayan nasararta don shi ya ba ta hadin kai yake kuma karfafa mata gwiwa a ko yaushe.

"Da yake kuma ya yi ritaya, sana'ae ba karamin taimaka mana take ba," in ji Rukayya.

A yanzu haka, Rukayya ta yi rajistar kamfaninta da hukumar da ke yi wa kamfanoni rajista.

Labarai masu alaka