Yadda sana'ar dinka kayan amare ta zame min abin tinkaho

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon sana'ar dinka kayan amare

Latsa sama don kallon bidyon yadda Maimuna ta fara sana'ar:

Maimuna Abubakar Anka, wata mai sana'ar dinka kayan amare ce a jihar Kano kuma ta shaidawa BBC cewa ta karanta fannin ilimin na'ura mai kwakwalwa ne a jami'ar Bayero da ke Kano, amma sai ga shi ta rikide ta zama mai dinka tufafin zamani.

Maimuna ta ce tun ta na 'yar makaranta ita ta ke zana dinkunanta sai ta kai wa tela shi kuma sai ya dinka daidai da yadda ta zana masa.

Amma ta shaida mana cewa babban dalilin da ya sa ta bude wannan shago na dinki shi ne wani lokaci bayan ta kammala karatunta na jami'a sai ta nemi aiki a wani kamfani, ta ci jarabawar neman aikin amma aka hana ta aikin saboda ita mace ce.

"Ina ji ina gani aka hana ni yin aikin wai a cewar su ba zan iya aikin hada wayoyi ba tun da ni mace ce. Abin ya matukar kona min rai har na tunzura na bude shagon dinki," a cewarta.

Maimuna ta ce ta samu ci gaba da daukaka domin yanzu tana cikin kwararrun masu dinki a Najeriya da su ka yi fice.

Hakkin mallakar hoto Halima Umar

A kan batun ko ita take dinka kayan da kanta, maimuna ta ce ita dai nata zane ne kawai kuma ita take nuna yadda ake hadawa amma tana da teloli da suke yin dinkin.

Ta ce tana da abokan ciniki a kasashen duniya da jihohin Najeriya daban-daban.

Ta ce sau da yawa su kan aiko kayan nasu ne ta tashar mota sai a kawo mata ta dinka ita kuma idan gama dinkin sai ta aika masu ta tashar motar.

Ta ce shagon dinkinta na Malaabis ya samu karbuwa ne sakamakon amfani da kafar sada zumunta na Instagram, inda ya taimaka sosai wajen ganin dinkunanta sun yadu a gari da duniya ma baki daya.

Ta ce da ta fara wannan sana'a ba ta yi tunanin za ta samu karbuwa da cigaba irin wanda ta samu ba a yanzu, kuma ta san cewa ba wani abu ba ne ya sa dinkunan nata suka samu karbuwa ba a yanzu sai don dinkunanta masu kyau da tsari ne.

Tana yin dinkunan amare daga naira dubu arba'in ne zuwa abun da ya fi haka, "ya danganta da nauyin aljihun mutum, in ji ta.

Kuma ba a dinki kawai ta tsaya ba, ta na siyar da yadinan da ake dinka rigunar amare.

A game da zancen yanayin dinkuna da amare ke sawa yanzu masu nuna tsiraici, maimuna ta shaidawa BBC cewa ita a ganinta duniya yanzu ta sauyaa kuma kullun canzawa take yi. Don haka dole yanzu a rika ganin ya yi ya sauya.

Amma ta ce ita amare da yawa da take yi wa dinki ta na yi musu har da mayafi kuma hakan ba ya hana su yin kyau a ranar bikinsu.

Ta ce a kan samu matsaloli wajen abokan huldarta wajen riga ta yi musu yawa ko ta yi kadan, sannan kuma kayan aiki sun kara kudi a kasuwa don haka kudin dinki ma ya karu.

Maimuna ta ce ta na da burin nan gaba ta zama mai dinki ta fi ko wacce kwarewa a duniya gaba daya.

Nasarori

A yanzu haka Maimuna ta ce wannan sana'a tana matukar rufa mata asiri don har ta bude makarantar koyon dinki inda take da dalibai da dama da suke karatu kuma a ba su takardar shaida idan suka kammala.

Hakkin mallakar hoto Malaabis

Labarai masu alaka