Har yanzu giwaye na fuskantar barazana a Afrika

Adadin giwaye na ci gaba da raguwa a duniya
Bayanan hoto,

Adadin giwaye na ci gaba da raguwa a duniya

Wani rahoto kan cinikiyyar hauren giwa ta haramtacciyar hanya ya ce an kwato haure da dama a bara, sai dai an samu raguwa a yawan hauren giwaye da ake cirewa a duniya.

Kungiyar CITES da ke sa ido kan kasuwanci da ake yi da dabbobin da suke fuskantar barazana, ta ce an samu raguwa yawan hauren giwaye da ake cirewa a wurare da dama a Afrika.

Sai dai wakilin BBC ya ce kawo yanzu ana cigaba da kashe giwaye a nahiyar Afrika kuma ana cigaba da samun raguwa a yawan giwayen da ake da su a duniya.

Tan 40 na hauren giwa ne aka kwato a bara.

Karanta wasu karin labarai

Matsalar ta ragu sosai a gabashin Afrika, wadda ta rasa rabin giwayenta a cikin shekaru goma da suka gabata.

Shugaban kungiyar ta CITES , John Scanlon ya ce shiirin kare giwaye na kasashen duniya ya soma yin tasiri, amma ya ce ana bukatar karin matakai.