Twitter ya bullo da sabbin ka'idojin talla

Sabbin kaidojin yin tala na shafin Twitter Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabbin kaidojin yin tala na shafin Twitter

Shafin sada zumunta na Twitter zai kaddamar da wasu sabbin ka'idoji kan tallace-tallacen da ake yi a lokacin zabe.

Kamfanin Twitter ya ce ya dauki wannnan mataki ne domin maida martani kan sukar da aka rika yi game da kutsen da ake zargin Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na Amurka a shekarar 2016.

An dai gano wasu shafuka 200 masu alaka da gwamnatin Rasha.

Amurka ta yi barazanar daukar mataki akan halayyar rashin gaskiya na kudaden da 'yan siyasa suke kashewa a shafukan sada zumunta.

A yanzu shafin Twitter zai dinga bada bayani a kan wanda ya biya kudin tallan da ya wallafa da yawan kudin da aka kashe da kuma masu amfani da shafin da ake son a ja hankalinsu.