'"Free Zakzaky har jikokinmu'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda 'yan shi'a suka gudanar da zanga-zangar neman a sako Zakzaky

Daruruwan 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Shi'a sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja domin neman gwamnati ta saki malaminsu Sheikh Ibraheem Zakzaky.

Baya ga haka 'yan kungiyar sun nuna adawa da yunkurin gwamnatin kasar na sa kwamitin da zai binciki abin da ya faru tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar a garin Zariya a shekarar 2015, ya zama a asirce.

Rikicin dai ya haddasa asarar rayuka da dama, kuma tun lokacin ne ake tsare da malamin duk kuwa da umarnin da kotu ta bayar cewa a sake shi.

Labarai masu alaka