Rahama Sadau ta nemi gafarar Ganduje da Sarki Sanusi II

Wani hoto daga wakar "I Love You" ta ClassiQ
Bayanan hoto,

Wakar "I Love You" ta ClassiQ ce ta jawo aka dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood

Shahararriyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.

Wannan batu ne ya jawo kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa, MOPPAN, reshen jihar Kano, ta koreta daga masana'antar a watan Oktoban bara.

A wata wasikar da ta aike wa MOPPAN, wacce BBC Hausa ta samu kwafinta, Rahama ta nemi afuwa kan abin da ta yi, tana mai cewa "kuskure ne," kuma za ta "kiyaye gaba".

Jarumar, wacce korar tata ta sa ta koma fitowa a fina-finan Nollywood, ta kuma tabbatar wa Nasidi Adamu Yahaya cewa hakika ta nemi gafara kan rungumar mawaki ClassiQ da ta yi.

Sai dai wannan wasika da Rahama ta rubuta tamkar ta yi amai ne ta lashe, saboda ko a watan Yulin da ya gabata ta shaida wa BBC cewa babu wanda ya dakatar da ita daga Kannywood.

Shugaban MOPPAN Kabiru Maikaba ya shaida wa BBC cewa kungiyar za ta sanar da matsayin da ta dauka a kan afuwar da jarumar ta nema bayan shugabanninta sun tattauna a hukumance.

Amma ya ce kungiyar za ta yi kokarin kwatanta adalci ga Rahama a duk wani mataki da za ta dauka.

Bayanan bidiyo,

Ba wanda ya dakatar da ni —Rahama Sadau

Abin da wasikar ta kunsa

Ta rubuta cewa: "An kai shekara daya ke nan tun faruwar wannan lamari, na yi iyakar kokarina don na nutsu sosai ta yadda ba za a bai wa kalamaina wata ma'ana ta daban ba kamar yadda kafofin yada labarai da wasu mutane suka dinga yi a baya.

"Ni 'yar-Adam ce wacce ba ta kubuta daga aikata kuskure ba, kuma ni 'ya ce wadda za a iya yi wa gyara; ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu shirya fina-finai, da dukkan al'ummar arewacin Najeriya da ma dukkan masu kallo da su gafarce ni," in ji Rahama.

Kazalika, jarumar ta yi magana a wasu gidajen rediyo na jihar Kano, inda ta jaddada neman gafarar musamman ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da kuma gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A karshen wasikar dai Rahama ta yi alkawarin bin dokokin da kungiyar ta shimfida.

Karanta wasikar neman gafarar da Rahama Sadau ta rubuta

Asalin hoton, Rahama Sadau/Moppan

Bayanan hoto,

Rahama Sadau ta yi alkawarin bin doka a nan gaba

Asalin hoton, TWITTER

Bayanan hoto,

Wannan batu na Rahama Sadau ya jawo ce-ce-kuce sosai a Kannywood