Ya kamata a fito zabe - Shugaban Kenya

Zanga zanga kan zaben shugaban kasar Kenya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zanga zanga kan zaben shugaban kasar Kenya

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya yi kira ga mutane a kan su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kuma su kada kuria a zaben shugaban kasa da za a sake yi a ranar Alhamis.

Mista Kenyatta ya ce an tura jami'an tsaro zuwa sasan kasar daban-daban kuma ya yi gargadin cewa ba zai amince da tashe tashen hankula ba.

Jagoran 'yan hammaya, Raila Odinga , ya nemi magoya bayansa a kan su kaurace wa zaben , saboda ya yi amannar cewa ba sahihin zabe ba ne.

Zaben zai gudana ne bayan da kotun koli ta kasa saurarar karar da wasu suka shigar a gabanta, inda suka nemi a dage zaben.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jagoran 'yan hammaya Raila Odinga

An yi taho-mu-gama tsakanin 'yan sanda da magoya bayan Mista Odinga a lardin Kisumu.

Gwamnatin kasar ta bayar da hutu a jiya Laraba domin mutane su samu damar yin tafiya zuwa wuraren da aka yi mu su rajista.

Zaman doya da manya da ake yi tsakanin 'yan siyasa na janyo fargaba kan barkewar tashe-tashen hankula.

Mutum fiye da 1600 ne suka mutu, yayin da dubbai sun rasa matsugunansu a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi a 2007.