'Babu wani aibu a auren wuri'

Auren wuri ba shi da aibu a cewar wasu iyaye Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Auren wuri ba shi da aibu a cewar wasu iyaye

Yayin da a ranar Laraba ne aka kamala taron da ake a kan yadda za a kawo karshen auren wuri a yammacin Afirka da tsakiyar Afrika, wasu iyaye a Najeriya sun ce ba bu wani aibu tattare da auren wuri.

Sun ce auren wuri na da alfanu sosai saboda yana hana matasa aikata dabi'ar da ba ta dace ba.

Malam Muhammad Sadisu Rajab, mahaifin wasu 'ya'ya mata ne a Najeriya, kuma a cewarsa barin auren wuri na kawo matsaloli da suka fi yoyon fitsari illa.

Taron da aka yi a Dakar babban birnin kasar Senegal ya samu halartar shugabannin kungiyoyin agaji, da jami'an gwamnati da shugabannin addinai da na al'umma da kuma hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Mahalatan taron na son su hana aurar da yara mata kafin su kai shekaru 18

Labarai masu alaka