Za a kona gawar Sarkin Thailand shekara guda bayan rasuwarsa

The royal chariot Hakkin mallakar hoto AFP

Dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Bangkok don martaba gawar Sarkin Bhumibol Adulyade.

Sarkin ya mutu ne a watan Oktobar shekarar 2016, yana da shekara 88.

An fara bukuwan binne marigayin ne a ranar Laraba kamar yadda tanadin addinin Buddha ya shinfida.

Galibin gidajen da ke birnin an lullube su da kyallaye masu ruwan dorawa, yayin da jama'a suka sanya bakaken tufafi.

A ranar Alhamis ne za a kona gawar sarkin, bayan dansa ya cinnna mata wuta a fadarsa.

Ana hasashen cewa taron jana'izar ya samu halartar kimanin mutum 250,000.

Shekara daya ke nan yanzu da aka fara ayyana zaman makoki a kasar tun bayan rasuwarsa a ranar 13 ga watan Oktoban bara.

Labarai masu alaka

Karin bayani