Yadda mata ke shiga matsala sakamakon zubewar ciki

silhouette of a woman
Image caption Yawancin mata ba sa kaunar yin magana game da zubar da ciki

Daya a cikin mata uku za ta zubar da ciki a tsawon rayuwarta, amma abu ne da ba a cika yin maganarsa ba.

Ga wasu, yanke hukuncin zubar da cikin na da tsananin tashin hankali kuma yana iya zama a zuciyar mutum har abada. Ga wasu kuwa, yana karfafa masu gwiwa, kuma yasauya masu rayuwa.

Kuna ta ba mu labarin zubar da cikinku shekaru hamsin bayan da a ka sanya dokar zubar da cikin a shekarar 1967.

'Na samu sassauci, na ji farin ciki kuma na ji dadi'

Louise a Landan: "Lokacin da na ke da shekara 23 na gane ina da ciki. Ban taba yin da-na-sanin zubar da ciki ba. Ya taimaka wajen tabbatar min da cewa lallai ba na so in haihu".

"Daga farko da ban ga al'adata ba, sai na yi tunanin ko saboda ina cikin damuwa ne. Na ji kamar ina da lalurar rashin lafiyar da mata ke yi kafin zuwan al'adarsu.

"Sai wata rana a wajen aikina, sai da na kwanta a tantagaryar kasa saboda tsananin gajiya. Na shiga tunanin abun da ya same ni, sai kawai abun ya fado min a rai.

"Na yi gwaji domin duba juna biyu lokacin hutun cin abincin rana a wajen aiki. Ina ganin gwajin ya nuna cewa ina da juna biyu, sai na fara jijjiga da karfi. Na so in yi dariya da kuka duk a lokaci daya.

"Wata abokiyar aikina wacce ta dade tana neman haihuwa ta fara murna da na gaya mata cewa ina da juna biyu. Amma ko da na gaya mata ni a wurina ba abun farin ciki ba ne ta fahimce ni. Sai kawai ta rungume ni".

"Mijina ya kyale ni na dau shawarar ni kadai. Ba mu taba tattaunawa a game da zubar da cikin ba. Kawayena na kusa-kusa sun bani goyon baya".

"Likitana kuwa ya nuna halin ko in kula. Na tattauna sau biyu da wasu malaman asibiti kafin a ka zubar da cikin.

"Ba su taba tambayata ko abun da na ke yi daidai ne ba. Na tabbata. Aikin zubar da cikin na da matukar zafi saboda na zabi a yi min aikin ba tare da an yi min allurar kashe zafi ba, amma ba a dade ana yin aikin ba".

"Da a ka yi aikin, damuwar da na shiga kafin a yi aikin ta tafi. Na samu sassauci, na ji farin ciki kuma na ji dadi."

'Ya jefa ni halin bakin ciki'

Beth (ba sunanta na gaskiya ba)na zaune a Ingila:

"Shekaruna 17 lokacin da na samu juna biyu, kuma na zubar da shi a watan Fabrairu".

"A yanzu haka ina da ciki kuma wannan karon ba zan zubar ba, ina farin ciki da shi."

"Lokacin wani bikin kirisimeti ne, kowa na ta annashuwa, ni kuwa ina ta rashin lafiya. Na yi tunanin saboda mu na ta shan barasa ne, sai wani ya zolaye ni ya ce ko dai juna biyu ne da ni. Sai ko na gano juna biyun ne da ni."

"Saurayina bai ce komai ba dangane da juna biyun, kuma ya kyale ni na dauki matakin da na so. Mahaifiyata kuwa ta natsu, kuma ta ce in yi abun da nake so in yi."

"Amma mutane da dama sun ta gaya min cewa na yi yarinta kuma ban shirya haihuwa ba. Na fuskanci matsin lamba dangane da zubar da ciki. Ya jefa ni cikin halin bakin ciki."

"Na fuskanci tsananin damuwa bayan da na zubar da cikin saboda raina ya baci sosai. Na ji kamar na dauki matakin da bai dace ba kuma babu abun da zan iya yi dangane da hakan.

"Likitan ya bani magunguna da shawarwari. Dama can ina da ciwon damuwa da rashin kwanciyar hankali sai hakan ya sa ciwon nawa ya kara tsanani.

"Yanzu da nake dauke da wannan cikin, mahaifiyata da saurayina su na ganin in yanke hukunci da kaina."

"A watan Afrilu zan haihu, kuma na kagu lokacin ya yi."

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Na shiga damuwa kan yanke hukuncin da ya dace

'Ya kamata a rika ilmantar da mutane cewa zubar da ciki ba laifi bane"

Harriet a Kudu Maso Gabashin Ingila:

"Abu ne da ba shi da dadi amma kana koyar darasi daga wadannan abubuwan."

"Shekarata 20 lokacin da na zubar da ciki."

"Idan na ga 'ya'yan kawayena ko kuma 'ya'yan 'yan'uwana sai na rika tunanin da yanzu ni ma ina da jariri dan wata uku."

"Da na fara gane cewa ina da ciki na yi murna kuma na nuna kulawa- na yi tunanin wannan jaririna ne kuma babu wanda zai iya karbe shi."

"Mahaifiyar kawata ta taimaka min kuma ta ce ni ma danginta ce amma ni na sa nawa iyalin, ko kuma makamancin hakan."

"Ba ni da wani zabi. Mahaifina ya ce zabina ne amma ba zai iya tallafa min da kudi ba. Da gaske ne, gaskiya ya gaya min. Na yi tunanin zan zamo mai son zuciya idan na ce zan haihu. Ya kamata a ce da ya samu kulawa daidai gwargwado."

"Uban dan ba ya son cikin. Na ji haushinsa saboda matsayin da ya sani a ciki. Sai ya zamo kamar an takura ni a sako, kuma ba zan iya haihuwar dan ba saboda bani da halin kula da shi."

"Abu ne mai matukar ban takaici farfadowa daga allurar baccin. Cikin ya wuce wata uku don haka sai da aka yi min tiyata.

"Abu ne marar dadi. Na farka da zummar sanin abun da ya faru da jikina, da kuma rashin son sanin abun da ya faru."

"A ko yaushe na kasance cikin kuka kuma yanzu ina tunanin wannan shi ne abun da na yi wa dana na fari."

"Hukumar Kula da Lafiya ta Kasar (NHS) ta bani tallafi sosai kuma ta bani damar sauya ra'ayina. Ya kamata a rika ilimantar da mutane a kan cewa zubar da ciki ba laifi ba ne kuma zabin mace ne amma dole a ba ta tallafi sosai."

"Akwai kyama sosai da a ke alakantawa da zubar da ciki."

Labarai masu alaka