Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou yayin wani taron kungiyar ECOWAS a birnin Niamey ranar Talata

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou yayin wani taron kungiyar ECOWAS a birnin Niamey ranar Talata

Bayanan hoto,

'Yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Sheikh Ibraheem Zakzaky lokacin da suka yi wata zanga-zanga domin neman sako malamin a Abuja ranar Laraba

Asalin hoton, DG Media

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da uwargidansa Hafsa yayin da yake komawa Kano daga Abuja bayan dawowa daga kasar Birtaniya a makon jiya

Asalin hoton, Kaduna Sate Government

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai yayin da yake gaishe da Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris gabanin fara taron majalisar tsaron jihar ranar Talata

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya gana da shugabannin majalisar dokoki ta kasar a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis

Asalin hoton, Kaduna State Goverment

Bayanan hoto,

Wadansu da ake zargi da satar mutane don neman kudin fansa wadanda aka kama a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Kano ranar Juma'a

Bayanan hoto,

Wani dan kama lokacin da ake bikin bude wani asibitin kiwon lafiya a matakin farko, wanda Hukumar Tarayyar Turai ta gina a Garin Gui da ke Abuja, ranar Juma'a

Asalin hoton, Kaduna State Goverment

Bayanan hoto,

Sanata Kabiru Gaya tare da Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai lokacin da kwamitin ayyuka na majalisar dattawan kasar ya kai wa gwamnan ziyara a Kaduna ranar Laraba

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wadansu gwamnonin kasar a kan hanyarsu ta zuwa masallacin Juma'a a fadar shugaban da ke Abuja ranar Juma'a