'Har Cuba na je neman magani ban dace ba'

Vitiligo
Image caption Wasu lokuta masu fama da cutar mele kan fuskanci tsangwama

Wata mai fama da cutar mele a Najeriya ta bayyana damuwa saboda rashin maganin cutar, wadda ta ce ta kai ta har zuwa kasar Cuba amma ba ta dace ba.

Matar wadda ba a bayyana sunanta ba, ta ce tun cikin shekarar 1995 ta fara amfani da wani magani Melaganina da likitoci suka ba ta, da ya yi aiki.

A cewarta ya kamata ta sake komawa ganin likita bayan shekara guda amma ba ta samu zarafin yin haka ba, sai bayan shekara biyar ta koma.

"Sun kara ba ni wani magani sai abin kamar ma yana karuwa" maimakon raguwa, don haka "sai na zo na daina magani ma, don gaji."

Hakkin mallakar hoto CBS
Image caption Cutar mele dai kusan takan fito a kowanne sashe na fatar jiki

Cutar mele dai tana dade wa mutum wani sashen jiki, inda wajen zai yi dau kamar kuna.

A cewar shafin intanet na Gidauniyar kula da cutukan fata ta Burtaniya (British Skin Foundation) mele cuta ce ruwan dare da ke shafar kimanin kashi 1 cikin 100 na al'ummar duniya.

"... masu fama da cutar mele sun fi sauran mutane yiwuwar kamuwa da wasu cutukan, da ake samu ta irin wannan hanya, da kuma sauran sassan jiki irinsu makwallato."

Mai fama da wannan cutar ta fada wa BBC cewa melen ba ya yi mata ciwo, amma dai takan fuskanci tsangwama musammam lokacin tana yarinya.

Ta ce ko da yake akan haifi wasu, da wannan cuta amma ita ta kamu da ita ne sakamakon wata allura da ta gama aiki.

"Ina 'yar shekara shida (lokacin) aka ban allurar a hannu kuma daga nan sai cutar ta fara bayyana," in ji ta.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Mai sana'ar tallata tufafi Winnie Harlow 'yar kasar Kanada na daga cikin fitattun mutanen da ke fama da wannan cuta a duniya

Gidauniyar tallafa wa masu cutukan fata ta Burtaniya ta ce cutar mele wani lokaci tana warkewa da kanta, kuma akan samu wasu magunguna da ke rage karuwarta a jiki.

"Ko da yake, babu wani tabbaci na samun maganin da ke warkar da ita."

Labarai masu alaka