Korar su Babachir ba ta isa ba – Rafsanjani

Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Wannan ne karon farko da shugaban ya kori wani babban jami'i da ke gwamnatinsa

A ranar Litinin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami Sakataren Gwamnatin kasar Babachir Lawal, inda ya maye gurbinsa da Boss Mustapha.

Hakazalika shugaban ya kori shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasar (NIA) Ambassador Ayo Oke.

Wannan ne karon farko da shugaban ya sallami wani babban jami'i a gwamnatinsa kan zargin almundahana.

Sai dai jim kadan bayan sanarwar dakatarwar ne jama'a a kasar suka rika bayyana ra'ayoyinsu musamman a kafofin sada zumunta

Ade Banqie wani dan kasar ne wanda ya ce sun "zuba idanu su ga ko shugaban zai mika Babachir Lawal ga hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar tu'annati (EFCC)."

"Muna neman karin haske. Don kora ba ta wadatar ba," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Hakkin mallakar hoto Twitter/ Banky

'Dole a hukunta su Babachir'

Akwai manyan jami'an tsohuwar gwamnatin kasar da har yanzu hukumar EFCC take rike da su kamar Olisa Metuh da Kanar Sambo Dasuki da Diezani Alison-Madueke da sauransu, bisa zargin almundahana.

Auwal Musa Rafsanjani, wakili a kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transperancy International ya shaida wa BBC cewa:

"Korar da akai musu ba za ta gamsar da mu ba, lalle duk wanda aka kama da laifi ya kamata ne a hukunta shi. Don ya zama darasi"

Ya kara da cewa: "Idan kawai aka tsaya a kora, to sauran mutane za su rika korafi suna cewa to damme ga wadansu mutane ana musu shari'a, amma wadannan fa?"

"Dole ne idan ana so a yi yaki da cin hanci da gaske sai an hukunta wadannan mutane," in ji shi.

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ce ba zai iya cewa "eh ko kuma a'a ba" game da batun gurfanar da mutanen da ake zargi da almundahanar.

"Ai hukunci doka ba magana ce ta shugaban kasa ba. Idan sai an jira sai shugaban kasa ya ce a kama wancan, ko a saki wancan to ai ba za a bi doka ba ke nan," in ji shi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Buhari ba ya yin rufa-rufa – Garba Shehu

Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron cikakkiyar ganawar da BBC ta yi da shi ta manhajar Skype.

Sai dai Malam Kabiru Lawanti wanda ke koyarwa a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya ya ce batun ba haka yake ba.

Ya ce abin da kakakin shugaban kasar ke ikirari zai yiwu ne kawai idan a ce hukumomin gwamnati suna aikinsu yadda ya dace.

Lawanti ya ce "Garba Shehu ya yi kokarin kare bangaren shugaban kasa ne kawai. Idan aka yi la'akari da abubuwan da suka faru a kwanakin baya."

"Yawancin mutanen da ake zargi da babakere a kan dukiyar al'umma hukumar EFCC tana musu dirar mikiya ne a gidajensu. Su kamu su, san nan su fara bincike."

"Abu biyu 'yan Najeriya suke son ganin a wannan lokaci," kamar yadda ya ce.

"Na farko ya kamata hukumar EFCC ko ICPC ta kama su. Kuma ta kwace kadarorinsu, daga nan sai a ci gaba da bincike kan al'amarin."

Ya ce abu na biyu "idan duka wadannan ba su samu ba, to dole ne hukuma ta gurfanar da su a gaban kotu tun da akwai sakamakon binciken da aka yi a kansu. Idan an same su da laifi sai a hukunta su."

"Wannan shi ne abin da duk wani dan Najeriya mai son ci gabanta zai so a yi, amma ba maganganun siyasa ba," in ji Lawanti.

Labarai masu alaka