Rasha za ta gina tashar wutar lantarkin Nukiliya a Nigeria

Wata tashar wutar lantarki a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a gina sabbin tashoshin ne a jihohin Kogi da kuma Akwa Ibom

Kasar Rasha ta kulla yarjejeniyar ginawa da tafiyar da sabuwar tashar makamashin Nukiliya a Najeriya, kasar da take fama da matsalar karancin hasken wutar lantarki.

Wani kamfanin kasar Rasha, mai suna Rosatom, shi ne zai yi aikin gina tashar, wadda a zangon farko za ta samar da Megawatt 1000.

Wani jami'i a hukumar kula da makamashin Nukiliyar ta Najeriya wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa BBC batun gina sabuwar tashar.

"Za a samar da tashohi guda biyu ne a jihohin Kogi da kuma Akwa Ibom kuma kasar Rasha ce za ta fi zuba kudi a aikin, amma za a fara gina guda daya ne saboda yadda gina tashar yake tsada," kamar yadda ya ce.

Ya ce ana fatan fara gina tashar a tsakanin "shekara daya zuwa biyu da ke tafe amma ba a sanya ranar farawa ba tukuna."

A shekarar 2015 ne kasar ta fara tattaunawa da kamfanin Rosatom don samar da tashohin wutar lantarki hudu a lokacin a kan kudi dala biliyan 20.

Megawatta 4,500 na wutar lantarki Najeriya take samarwa a halin yanzu, a kasar da ke yawan al'ummar da ya kai kusan miliyan 200.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka