Ana daf da sanar da wadda ta lashe Gasar Hikayata ta BBC

Alkalan Hikayata a lokacin da suke tantance labaran gasar
Bayanan hoto,

Alkalan Hikayata a lokacin da suke tantance labaran gasar a ofishin BBC Hausa

A karshen makon nan ne za a sanar da labaran da suka yi nasarar lashe gasar rubutun kagaggun labarai ta mata ta BBC Hausa.

Alkalan gasar dai za su zabo labarai ukun da suka fi sauran ne da kuma wasu 12 da suka cancanci yabo daga cikin labarai 25.

Marubuciyar labarin da ya zo na daya za ta samu kyautar $2,000 (kimanin naira 700,000) da lambar yabo.

Sai wacce ta zo ta biyu za ta samu $1,000 da lambar yabo; yayin da wadda ta rubuta labarin da ya yi na uku za ta karbi kyautar $500 da lambar yabo.

Sauran labarai 12 da suka cancanci yabo kuwa za a karanta su a shirye-shiryenmu a watanni masu zuwa.

Sashen Hausa na BBC ya kirkiro wannan gasa ne dai a bara da nufin bai wa mata damar bayyana abubuwan da suka fi ci musu tuwo a kwarya.

Sai ku kasance da Sashen Hausa na BBC ranar Asabar 4 ga watan Nuwamba a rediyo da intanet da kuma shafukan sada zumunta don samun bayani game da labaran da suka yi nasara.