An kashe mutum 10 a cikin tasi a Afirka ta Kudu

Afirka ta kudu

Asalin hoton, Getty Images

A kalla mutum 10 ne suka mutu a Afirka ta Kudu bayan da aka yi wa motar da suke ciki kwanton bauna a yankin KwaZulu Natal da ke bakin gabar teku.

Shugaban kungiyar 'yan tasi na yin balaguro ne tare da dogaransa, lokacin da aka budewa motocinsu biyu wuta a garin Ladysmith.

Dukkan mutane biyar da ke cikin motocin sun mutu, kuma motar tasu ta yi taho mu gama da wata motar safa ta daukar fasinja inda wasu mutum biyar da ke ciki su ma suka mutu.

An sha samun matsalar tare motocin haya a hanyoyin yankin KwaZulu Natal.

"Ga dukkan alamu wannan hari na da halaka ne da wani rishin jituwa tsakanin wasu kungiyoyin 'yan tasi guda biyu," a cewar 'yan sanda.

Sai dai 'yan sanda sun ce duk da cewa babu wani karin haske game da lamarin, za a ci gaba da bincike.