Kun san rawar da Amokachi ya taka a fagen tamaula?

  • Abdulwasiu Hassan
  • BBC Hausa, Abuja
Amokachi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daniel Amokachi yana cikin 'yan wasan da suka fara kai Najeriya gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 1994

Wannan makala ce da muka rubuta don amsa tambayoyinku a kan abin da kuke son sani game da tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Daniel Amokachi. A sha karatu lafiya.

An haifi Daniel Owefin Amokachi ne a ranar 30 ga watan Disamba a shekarar 1972 a garin Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Daniel Amokachi ya ci gasar cin kofin nahiyar Afirka sau daya matsayinsa na dan wasa, kuma sau daya a matsayinsa na mataimakin kocin Najeriya.

Da alama 'ya'yansa biyu wadanda tagwaye sun bi sahunsa domin su ma yanzu suna taka leda yadda ya kamata.

Mene ne tarihin Daniel Amokachi kuma daga ina ya fito?

Wanan na cikin tambayoyin da masu bibiyar shafinmu na BBC Hausa suka fi tambaya, ciki har da Ayyuba Yahaya da kuma Isma'il Wudil.

Daniel Amokachi, dan asalin jihar Kaduna ne wadda take yankin arewacin Najeriya.

Lokacin da yake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees ta Kaduna ne ya ja hankalin kocin Super Eagles na lokacin, Clemens Westerhof.

A shekarar 1989, Amokachi ya taimaka wa kungiyar Ranchers Bees ta lashe kofin gasar kungiyoyin kwallon kafa na Afirka ta yamma.

Bayanan hoto,

Amokachi yayin da ya kawo ziyara ofishin BBC kwanakin baya

Daga nan ne Clemens Westerhof ya saka Amokachi cikin 'yan wasan da suka wakilci Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka gudanar a birnin Aljiyas na kasar Aljeriya a shekarar 1990.

Najeriya ta samu ta kai wa ga wasan karshe a gasar, amman ta sha kaye a hannun masu masaukin baki, Aljeriya, da ci daya da nema duk da cewa an saka Amokachi a wasan.

Daga nan ne tauraruwar dan wasan ta kara haskakawa.

Duk da cewa dan kwallon yana da shekara 16 ne a wancan lokacin, amma 'yan kallo sun ji dadin irin zafin naman da yake nunawa a hare-haren da ya yi ta kai wa a wasannin da ya buga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daniel Amokachi ya yi suna a gasar cin kofin FA na Ingila a shekarar 1995

Wasan shi a Turai

Daga nan sai bangaren matasa na kungiyar kwallon kafa ta Club Bruges da ke Belgium ta saye shi.

Amman ba da jimawa ba aka mayar da shi bangaren manyan 'yan wasan kungiyar domin salon taka-ledarsa ya gamsar da jagororin kungiyar kwallon kafar.

Nan da nan nasarorin da ya samu a gasar cin kofin Belgium da kuma ta gasar Turai suka sa ya yi fice, kuma aka fara kiranshi "D Bull" domin irin salon wasansa.

Kuma ya samu kyautar Ebony Boot wato kyautar da ake ba bakin fata da ya fi iya taka leda a kasar Belgium.

Lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka

Bayan ficen da ya yi a tawagar Super Eagles a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 1990.

Amokachi bai yi kasa a gwiwa ba a gasar da aka yi bayan shekara hudu, Tunisia 1994, da kuma gasar cin kofin duniya da aka yi a Amurka a shekarar 1994, inda ya yi nasarar zura kwallaye biyu a raga.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amokachi yana cikin 'yan wasan da suka lashe gasar cin kofin Afirka a shekarar 1995

A wasan da Najeriya ta doke kasar Girka, da ta ci da 2-0, Amokachi ya ci wata kwallo mai kayatarwa inda ya wuce masu tsaron baya hudu kuma ya jefa kwallon cikin raga daga yadi 25.

Akwai rade-radin cewar kwallon da ya ci Girkar ce ta sa kungiyar kwallon kafa ta Everton da ke gasar Firimiya ta saye shi daga baya.

Sai ya koma Everton, abubuwa ba su tafi yadda yake so daga farko ba.

Amman bayan ya zauna a benci a kakarsa ta farko a Everton, lamarin ya sauya musamman ma a gasar FA Cup ta shekarar 1995 lokacin da Joe Royle ke jagorancin kungiyar kwallon kafar.

Amokachi ya ci kwallo biyu a nasarar da Everton ta samu kan Tottenham da 4-1 a wasan dab da na karshe a gasar FA cup ta shekarar 1995.

Yanayin yadda ya sa jiki a wasa da kuma yadda yake gudu ya sa magoya bayan kulob din suka rada masa sunan "Amo-Taxi".

Ya ci kofin FA Cup da Everton a wancan shekarar kafin abubuwa su sake tsananta.

Dan wasan ya kasance daya daga cikin 'yan wasan masu yawan shekaru da suka wakilci Najeriya a gasar Olympics da aka yi a birnin Atlanta a shekarar 1996.

Ya ci wa Najeriya kwallo ta biyu a wasan karshe, inda ta doke Argentina 3-2.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amokachi (daga dama) tare da tsofaffin kocin Najeriya biyu Augustine Eguavoen da kuma Samson Siasia

Duk da cewa mutane suna ganin wannan na daya daga cikin abubuwan da za ayi ta tuna Amokachi da su, dan kwallon yana ganin lokacin duk da ya shiga filin wasa a matsayinsa na dan wasan kwallon kafa, lokaci ne da yake tunawa da su.

Najeriya ta samu ta ci wannan wasan, kafafan yada labarai suna ganin "Amokachi ne ya yi tsayuwar daka."

Ba da jimawa ba, Amokachi ya bar Everton zuwa kungiyar kwallon kafa ta Besiktas da ke Turkiyya.

Ya taimaka wa kungiyar ta lashe kofin Turkiyya a kakarsa ta biyu.

Duk da cewa an samu rashin jituwa tsakaninshi da kocin kulob din, John Toshak, Amokachi ya ci gaba da zamansa a kungiyar.

A wancan lokacin dan wasan gaban ya ce: "an sanni a ko ina a duniya yanzu. Saboda haka ba wai ina wasa domin son a sanni ba ne."

"Ina wasa ne saboda kudi. Ina da iyalin da nake kulawa da su, manyan yara biyu da kuma matar da ya zama dole in yi tunani kan makomarta.

Raunin da ya ji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amokachi bai taka wa Super Eagles irin rawar da ya taka mata a da a ba a gasar cin kofin duniya ta shekarar 1998

Amman da aka je gasar cin kofin duniya da aka yi a Faransa a shekarar 1998, sai Amokachi ya samu matsala.

Maikamakon yadda ya taka rawar gani a gasar 1994, gudumawar da ya bayar mai karfi ita ce kwallon da ya bai wa Victor Ikpeba ya ci Bulgaria a daya daga cikin wasannin zagayen farko na gasar.

A wani lokacin da ake atisaye kafin wasan karshe a zagaye na farko inda Najeriya za ta kara da Paraguy, sai gwiwar Amokachi ta goce, kuma aka cire shi daga cikin 'yan wasan da za su wakilciu Najeriya a wasa na gaba.

Daga baya anyi masa tiyata a gwiwar, kuma ya dan dade bai taka leda ba.

A farkon shekarar 1999 an ba shi kyaftin din Super Eagles, amman bai samu cikakken lafiyar buga wa Najeriya wasa ba.

Bayan ya koma Turkiyya, sai ya mayar da hankali kan tallan kayan kawa kamar yadda matarsa 'yar Tunisiya take yi.

Besiktas ba ta sabunta kwantiranginsa ba bayan ya kare a shekarar 1999.

Da Najeriya ta fara shirin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2000, an gayyaci Amokachi, amman bai samu ya buga wasa ko daya ba.

Yadda ya zama koci

Daga nan Amokachi bai sake taka wani rawan azo a gani a kwallon kafa ba a matsayinshi na dan wasa.

Ya yi aiki a matsayin kocin kungiyoyin kwallon kafa na gasar Firimiyar Najeriya irin su Nasarawa United da Enyimba.

Ya yi aiki a matsayin mataimakin kocin Super Eagles a karkashin Berti Vogts, amman ya bar mukamin a shekarar 2008.

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto,

Daniel Amokachi da Stephen Keshi sun ci gasar cin kofin nahiyar Afirka a matsayin 'yan wada da kociyoyi

Amokachi ya yi aiki da marigayi Stephen Keshi a matsayin mataimakin kocin Super Eagles kuma sun lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013.

Da ya bar Super Eagles ya zama kocin kungiyar kwallon kafa ta JS Hercules da ke kasar Finland.

A yanzu kuma tsohon dan wasan ya zama daraktan dabarun kwallon kafa na kungiyar.

Sai dai kuma har yanzu Amokachi yana da burin zama kocin Super Eagles.

Game da burinsa na zama kocin Super Eagles tsohon dan wasan Najeriyar ya ce:

"Komai lokaci ne Allah, kuma abin da Allah Ya ce zai faru kuma haka zai zo."

Amman Amokachi ya yaba wa 'yan wasan Super Eagles na yanzu tare da jagoransu.

Ya ce ya kamata a yi ta yi musu addu'a domin su taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a shekarar 2018.