Yadda wani direba ya tattake mutane a America

Truck at scene of fatal attack in New York City on 31 October 2017

Asalin hoton, Reuters

A kalla mutum takwas ne suka mutu kuma, wasu 11 kuma sun jikkata bayan da wani mutum mai shekara 29 da haihuwa ya auka wa mutane a kan wata hanyar da aka tsara don masu kekuna a yankin Lower Manhattan na birnin New York na Amurka.

Wani dan sanda ya harbi mutumin bayan ya fito daga motar, kuma a halin yanzu ya shiga hannu.

Kafofin watsa labaran Amurka sun bayyana sunan mutumin - Sayfullo Saipov, wanda ya koma Amurka da zama a 2010 kuma mazaunin jihar Florida ne.

Magajin birnin New York Bill de Blasio ya ce wannan harin "abin takaici ne wanda aka kitsa domin hallaka wadanda ba su ji ba, ba su gani ba".

Babban kwamishinan 'yan sanda na New York, James O'Neill ya ce wadanda suka samu raunuka na "fama matsananciyar jinya, amma da alama za su samu sauki".

Ya bayyana yadda harin ya faru:

  • Jim kadan bayan karfe 3 na yamma agogon New York, maharin ya tuka motar da ya yi hayarta inda ya rika buge mutane a kan hanya.
  • Daga nan motar ta yi karo da wata motar daukan 'yan makaranta, kuma yara biyu da manyan mutane su biyu sun samu rauni.
  • Matukin motar sai ya fito daga motar yana rike da wasu ababe da suka yi kama da bindigogi guda biyu, kuma ya rika maganganu da suka yi "kama da na masu kai harin ta'addanci".
  • A lokacin ne sai wani dan sanda da ke kusa da wurin ya harbe shi a ciki.
  • Daga baya 'yan sanda sun tafi da bindigogin da yake rike da su.
Bayanan bidiyo,

Masu ayyukan ceto a wurin harin

Akwai kekuna masu yawa da maharin ya tattake a wurin da aka kai harin.

Wani wanda ya shaida lamarin mai suna "Eugene" ya fada wa tashar talabijin ta ABC Channel 7 cewa ya hango wata farar motar daukar kaya tana bin hanyar a guje, kuma yana kallo ta rika banke mutane.

Ya kuma ce ya ji karar harbin bindiga sau tara ko 10.

Asalin hoton, CBS

Wani mutum mai suna "Frank" ya bayyana wa tashar talabijin ta NY1 cewa ya ga wani mutum yana zagaye wata mahada kuma ya ji karar harbi sau biyar ko shida.

"Na ga wani abu a hannunsa, amma ban iya tabbatar da ko mene ne ba. Sai dai na ji sun ce bindiga ce".

"Bayan 'yan sanda sun harbe shi, sai wurin ya rikice, aka yi ta guje-guje. Da na sake dubawa, sai na taras ya riga ya fadi kasa."

An sanar da shugaba Trump halin da ake ciki, in ji wata sanarwa daga bakin Sarah Sanders a Fadar White House.

Sakamakon haka, shugaba Trump ya aika da wasu sakonni biyu a shafinsa na Twitter, yana cewa:

  • A birnin New York da alama wani wanda kansa ba daidai yake ba, ya kai hari.
  • Jami'an 'yan sanda na kokarin shawo kan lamarin. BA DAI A AMURKA BA!
  • Kada mu bari ISIS ta farfado, ko ta shigo kasarmu bayan mun kayar da ita a Gabas ta Tsakiya da sauran wurare. Ya isa haka!