Hotunan harin birnin New York
Wani mahari ne ya tuka motar kaya har kan wata kebabbiyar hanya ta masu kekuna, kuma 'yan sanda sun ce harin na ta'addanci ne.

Asalin hoton, Reuters
Wannan ce motar da maharin ya tuka inda ya rika banke matafiya a kafa da wadanda ke kan kekuna a yankin Lower Manhatan na birnin New York, in ji 'yan sanda.
Asalin hoton, EPA
An kashe akalla mutum takwas, kuma wasu 11 sun ji munanan raukuka a sanadin wannan harin.
Asalin hoton, Reutes
Jami'ai sun ce daga baya maharin ya yi karo da wata motar 'yan makaranta.
Asalin hoton, AFP/Getty Images
'Yan sanda sun harbi mutumin bayan ya fito da wasu bindigogi guda biyu. Amma an gane cewa bindigogin na boge ne. Rahotanni sun ce shekarunsa 29, sunansa Sayfullo Saipov, wanda ya koma Amurka da zama a shekara ta 2010.
Asalin hoton, Reuters
An ba wadanda suka jikkata kulawar gaggawa a wurin kafin kai su asibiti.
Asalin hoton, Reuters
... wasu kuma an kai su asibitoci.
Asalin hoton, AFP/Getty Images
Jama'a da yawa sun razana da aukuwar wannan harin.
Asalin hoton, Reuters
Ana amfani da karnuka domin duba motoci a yankin.
Asalin hoton, Reuters
Nan take iyaye suka garzaya makarantu suna komawa dasu gida domin harin.
Asalin hoton, EPA
Magajin garin New York tare da manyan jami'ansa suna kokarin shawo kan lamarin