Ban taba ganin jam'iyya mai sakaci irin APC ba - Masani

APC NEC Meeting Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Taron kolin ya zo ne bayan an sha kiraye-kiraye da korafe-korafe tsakanin kusoshin jam'iyyar

Wani masanin kimiyyar siyasa ya ce shi da takwarorinsa da dama sun dauka cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi barci kuma ta kasa farkawa.

A cewarsa: "Ganin jam'iyyar ta dade ba ta yi taron kwamitin zartarwarta na kasa ba, sai a ranar Talata."

Dr. Abubakar Kari malami a Jami'ar Abuja, ya ce taron yana da matukar muhimmanci, don haka ne ma tsarin mulkin jam'iyyar ya yi tanadin gudanar da taron a kalla sau uku a shekara.

"A iya sanina ba a taba yin wata jam'iyya wadda take mulki a tarayya da jihohi, da ta yi sake irin APC ba," in ji masanin siyasar.

Taron kwamitin zartarwar jam'iyyar APC na ranar Talata ya zo ne bayan an sha kiraye-kiraye da guna-guni musammam tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

Ya ce: "Ka ga tun lokacin da aka kafa wannan jam'iyya, wannan taro na kwamitin kolinta, shi ne na uku da ta yi."

In ji shi hatta sauran rassa na jam'iyyar ba sa taro, shiru kawai ka ke ji. Abin da ya sa rigingimu suka yi ta barkewa a jihohi da kuma tsakanin gaggan jam'iyyar kan batutuwa da dama.

Dr. Kari ya ce nade-naden da Shugaba Buhari ya yi alkawarin yi nan gaba, abu ne mai kyau da zai yi tasiri kwarai da gaske.

Masanin na sharhi ne bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana takaici kan jinkirin da aka samu wajen nada mambobin kwamitocin gudanarwa a hukumomin gwamnatin tarayya.

Ya ce nan ba da dadewa ba zai yi sabbin nade-naden don amfanin jama'ar kasar.

Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Karon farko kenan da jam'iyyar APC ta yi taron kwamitin zartarwar a cikin wannan shekara

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a taron koli na jam'iyyar APC ranar Talata a Abuja.

Abubakar Kari ya ce akwai manyan kusoshi a jam'iyyar wadanda ke korafe-korafen cewa sun yi yaki sun kafa gwamnati amma har yanzu ba a yi da su.

"Za a iya cewa Buhari da mukarrabansa sun yi sake kwarai da gaske tun da akwai manyan hukumomin gwamnati masu muhimmanci wadanda aka bar su babu shugabanci," in ji Malamin Jami'ar.

A cewarsa wasu daga cikin irin wadannan hukumomi ma ba sa iya gudanar da ayyukansu a yanzu.

Ya ce gwamnati ba za ta tafi daidai ba, kuma ba za ta iya cimma burinta ba sai Buhari ya yi wadannan nade-nade.

Dr. Kari ya ce yin nade-naden zai share hawayen wasu 'ya'yan jam'iyyar APC da ke korafin sun wahalta wa Buhari babu amma ya yi biris da su.

Labarai masu alaka