Nigeria: Dokar hana kiwo a Benue ta fusata Fulani

Makiyaya
Bayanan hoto,

Wasu makiyayan sun yi na'an da dokar yayain da wasu suka ki amincewa da ita

A ranar Laraba ne dokar haramta yawo da dabbobi domin kiwo ya fara aiki a jihar Benue ta Najeriya wadda ta dade tana fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Dokar dai za ta tilasta wa dukkan mai kiwo ya tsugunar da dabbobinsa a wuri guda, yayin da ta tanadi daurin shekara biyar ga dukkan wanda ya saba mata.

Har ila yau, wanda ya saba wa dokar zai iya biyan tarar naira miliyan daya a maimakon dauri, ko kuma a daure shi tare da cin tararsa.

Kungiyoyin Fulani a jihar sun yi Allah-wadai da dokar, suna masu cewa ta take hakkin makiyaya.

Bayanan hoto,

Jihar Benue da ma wasu sassan Najeriya na fama da rikici tsakanin manoma da Fulani

Jihar Benue da ma wasu sassan Najeriya sun sha fama da rikici tsakanin manoma da Fulani, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Daruruwan mutane aka kashe a watan Fabrerun bara, abin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami'an tsaro su far wa maharan, wadanda aka zarga da cewa Fulani ne. Sai dai sun musunta.

Dokar, wadda gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya rattabawa hannu a watan Mayun da ya gabata, ta kuma amince da kafa wuraren kiwo a jihar.

Gwamnatin jihar dai ta ce ta kafa dokar ne domin hana aukuwar tashe-tashen hankula tsakanin Fulani Makiyaya da kuma manoma, wanda jihar ta sha fama da su.

Amma wani masanin tsaro Malam Kabiru Adamu, ya shaida wa BBC cewa dokar za ta kara ruruta zaman dar-dar tsakanin al'ummar jihar maimakon samar da zaman lafiya.

Daya daga cikin shugabannin Fulani a jihar ta Benue, Garba Gololo, ya shaida wa BBC cewa tuni aka fara aiwatar da wannan doka a safiyar ranar Laraba kamar yadda aka tsara.

Bayani game da dokar

Dokar dai ta tanadi hukuncin daurin shekara biyar ga duk wanda aka samu da laifin kiwo ba a wuraren da aka killace ba, ko kuma tarar naira miliyan daya ko duka biyun.

Bayanan hoto,

Dokar ta hana tafiya da dabbobi ba tare da aza abun hawa ba

Haka kuma duk makiyayin da aka samu da laifin jikkata wani zai fuskanci zaman gidan kaso na shekara biyu tare da biyan kudin asibitin majinyacin.

Idan kuma lamarin ya zo da karar kwana, za a tuhumi makiyayi da laifin kisan kai.

Hakazalika, a karkashin dokar an haramta yawo da dabbobi da kafa a fadin jihar, sai dai a dauke su a kan abin hawa.

Kuma duk wanda aka kama a karon farko za a ci shi tarar naira 500,000 ko daurin shekara daya ko kuma duka biyu.

Wanda aka kama a karo na biyu kuma zai biya tarar naira miliyan daya ko a daure shi daurin shekara uku ko kuma ya fuskanci duka biyun.

Sabuwar dokar da ta fara aiki ranar Laraba, ta kuma haramta mallakar bindigogi ko da lasisi ko babu lasisi, kuma ta ce duk wanda aka kama zai fuskanci tuhuma.

Dokar ta kuma tanadi daurin shekara goma babu tara ga duk wanda aka samu da laifin wawure fili, don lamarin ya kai ga mummunan jikkata.

Ko kuma ya fuskanci tuhumar kisan kai idan ya zo da karar kwana.

Duk wanda aka samu da laifin satar shanu ko wasu dabbobi zai fuskanci daurin shekara uku ko ya biya naira 100,000 a kan ko wacce dabba.

Bayanan hoto,

An dade ana samun rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Benue

Idan lamarin ya zo da raunata mutum kuma, wanda aka samu da laifi zai yi zaman wakafi na shekara biyar ko ya biya tarar naira 500,000 ko duka biyu.

Idan lamarin ya kai ga rasa rai, mutum zai fuskanci tuhumar kisan kai.

Duk wata dabbar da aka gani tana yawo a jihar za a kama ta, in ji dokar.

Idan mai ita bai zo ba bayan mako guda, za a yi gwanjonta ga jama'a kuma a zuba kudin a asusun gwamnati.

Gwamnatin ta jihar Benue dai za ta kafa wani kwamiti na musamman domin tabbatar da an bi wannan dokar.

Kafin a fara aiwatar da wannan doka dai majalisar dokokin jihar sai da ta kira taron jin bahasi inda ta gayyato masu ruwa da tsaki ciki har da shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta jihar, wadanda suka yi na'am da dokar sannan kuma suka shiga cikin kwamitin aiwatar da dokar.

Sai dai kuma kungiyar a matakin kasa ta bayyana shakkunta ga lamarin.

Kuma tuni wata kungiyar Fulani wato Miyatti Allah kautal-hore, ta shigar da kara tana kalubalantar dokar.

Najeriya kasa ce da ta shafe shekaru tana fama da matsalar rikicin makiyaya da manoma, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da kadarori.