Shugaban Nigeria ya rantsar da Boss Mustapha

Buhari da Boss Gida

Asalin hoton, Femi Adesina

Boss Gida Mustapha ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon sakataren gwamnatin Tarayya a Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya rantsar da Mista Boss a fadarsa a Abuja.

Sabon sakataren gwamnatin ya zauna ne kusa da kujerar mataimakin shugaban kasa kafin soma taron majalisar zartarwa bayan da ya karbi rantsuwa.

Kafin nada shi sakataren gwamnati, Boss Mustapha shi ne shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa na cikin gida wato NIWA.

Cikin wadanda suka halarci bikin har da gwamnan Adamawa Mohammed Jibrilla.

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya nada sabon sakataren gwamnatin kasar, bayan da ya kori Mista Babachir Lawal bisa zargin cin hanci da rashawa.

Mr Boss Gida Mustapha lauya ne, dan siyasa kuma dan kasuwa.

Kafin a ba shi wannan mukami na sakataren gwamnatin Najeriya, shi ne shugaban Hukumar Kula da Rafuffukan Najeriya, (NIWA).

Shi ne kuma sakataren kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC a shekarar 2015, kuma mamba ne na kwamitin amintattu na APC.

Asalin hoton, Femi Adesina