Sai an biya ni N1b kafin in ba da shaida a kotu-Jonathan

Olisa Metuh

Asalin hoton, Olisa Metuh Twitter

Bayanan hoto,

Ana dai tuhumar Olisa Metuh ne da karbar wasu kudade da suka kai naira milyan 400, ba bisa ka'ida ba

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukaci a bashi dala miliyan 2.7 wato naira biliyan daya kenan, kafin ya bayar da shaida kan shari'ar da ake wa tsohon kakakin jam'iyyar PDP, Olisah Metuh kan cin hanci da rashawa.

A ranar Talata ne lauyan Mista Jonathan Mike Ozekhome, ya ce kudin za su taimakawa tsohon shugaban kasar ne wajen daukar dawainiyar zuwansa da dogarawansa daga kauyensa na Otuke zuwa babban birnin Najeriyar Abuja.

Ana dai tuhumar Olisa Metuh ne da karbar wasu kudade da suka kai naira milyan 400, ba bisa ka'ida ba daga hannun Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro.

Ana zargin cewa an karkatar da wadannan kudade ne daga cikin kudin da aka kebe domin sawo makamai don yaki da kungiyar Boko Haram, amma aka yi amfani da su wajen yakin sake neman zaben Mista Jonathan a 2015.

Dukkan mutanen biyu, Mista Metuh da Sambo Dasuki, wadanda ake yi musu shari'a a wurare daban-daban, sun sanar da cewa Jonathan na da masaniya game da bayar da kudaden.

Lauyoyin Metuh na kalubalantar Jonathan da Dasuki da su bayar da hujja, to sai dai dukansu biyu ba su halarci kotu ba a makon da ya gabata.

Lauya Ozekhome ya ce, Jonathan ba shi ne mutumin da ya dace ya bayar da shaida a wannan lamari ba.

Lauyan ya kuma kara da cewa: 'idan har alkali ya kafe cewa sai Jonathan ya gabatar da shaida, to lallai ne kotu ta umurci Mista Metuh ya ajiye kudi naira biliyan daya da za su kasance kudin balaguron Jonathan din.

"Wadannan kudade za su kasance na balaguronsa, daga garin da yake Otuoke a kudancin Najeriya zuwa Abuja, ciki har da kudin da za a bai wa dogaran da za su raka shi don kula da tsaronsa," in ji lauyan.

Garin Otuoke dai da ke jihar Bayelsa na da nisan kilomita 680 zuwa Abuja.

An gudanar da bincike kan Jonathan da kuma wasu 'yan uwansa da iyalai da abokai da ake kai wa a kotu, game da zargin cin hanci da rashawa, tun bayan da ya fadi zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lauyan Jonathan ya ce kudin za su taimakawa tsohon shugaban kasar ne wajen daukar dawainiyar zuwansa Abuja