Kotu ta ki yarda a taso keyar Diezani

Diezani Alison-Madueke na daya daga cikin mata 'yan siyasa da suka yi fice a Afrika Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Diezani Alison-Madueke na daya daga cikin mata 'yan siyasa da suka yi fice a Afrika

A Najeriya, wata babbar kotun tarayya da ke Lagos ta yi watsi da bukatar tsohuwar ministar man fetur ta kasar, Mrs Diezani Alison-Madueke, inda take neman a taso keyarta gida Najeriya don a yi mata shari'a a kan zargin hallata kudaden haramun.

Lauyoyin Mrs Diezani sun nemi kotu ta tursasa wa ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, ya amince a kawo tsohuwar ministar zuwa Najeriya ta fuskanci shari'a maimakon ta ci gaba da fuskantar tuhuma a London.

Sai dai lauyan gwamnati Rotimi Oyedeop ya ce Mrs Alison-Madueke za ta iya fuskantar shari'a a duk lokacin da ta dawo Najeriya.

Da yake yanke hukuncin ranar Laraba, mai shari'a Rilwan Aikawa, ya yi watsi da bukatar tsohuwar ministar inda ya ce kokari ta ke ta kaucewa fuskantar shari'a.

Mrs Alison-Madueke na daya daga cikin mata 'yan siyasa da suka yi fice a Afirka bayan ta rike mukamin ministar mai, kuma ita ce mace ta farko da ta rike mukamin shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC.

Yanzu haka dai tsohuwar ministar tana zaman beli ne a Landan tun bayan da aka tsare ta a watan Okotobar 2015, bisa zargin aikata cin hanci da halatta kudaden haramun.

Tun daga lokacin ne Mrs Alison-Madueke mai shekara 56 ta yi ta fuskantar shari'a a Najeriya da Italiya da kuma kasar Amurka.

A baya-bayan nan ne wata kotu a Najeriya ta mallakawa gwamnatin kasar kadarori da wasu kudade na tsohuwar ministar da ake zargin ta wawure lokacin da take rike da mukamin ministar mai.

Sai dai ta sha musanta cewa an sace makuden kudaden mai ta hannunta a lokacin da take kan mukamin ministar mai.

Labarai masu alaka