Niger ta nemi taimakon Amurka

Jiragen sama marasa matuka za su taimaka wajan dakile ayuikan 'yan ta'ada a iyakar Niger da Mali a cewar gwamnatin Niger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jiragen sama marasa matuka za su taimaka wajan dakile ayuikan 'yan ta'ada a iyakar Niger da Mali a cewar gwamnatin Niger

Gwamnati Nijer ta yi kira ga Amurka a kan ta fara amfani da jiragen sama marasa matuka, domin dakile ayuikan mayakan kungiyoyi masu ikirarin jihadi dake kan iyakar kasar da Mali.

Ta ce tana samun nasara a yakin da take yi da masu tsanannin kishin Islama amma har yanzu suna yi mata barazana a wasu yankunanta.

Ministan tsaron Nijar Kalla Mountari ya shedawa BBC cewa kawo yanzu ba bu wani yanki dake karkashin ikon 'yan ta'aada.

Kiran dai ya biyo bayan kisan da aka yiwa wasu sojojin Amurka 4 da kuma na Niger guda ,a wani harin kwantar bauna da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai mu su a kwanakin baya.

Babban hafsan hasoshin sojin Amurka ya ce za a gudanar da cikakken bincike a kan abinda ya faru lokacin da aka kai mu su harin.