An gurfanar da maharin Manhattan a gaban kotu

Ana tuhumar Sayfullo Saipov da goyon bayan kungiyar IS da ke ikirarin jihadi da kuma kashe mutum 8.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana tuhumar Sayfullo Saipov da goyon bayan kungiyar IS da ke ikirarin jihadi da kuma kashe mutum 8.

A gurfanar da dan Uzbekistan da ya koma Amurka wanda ake zargi ya afkawa mutanen da ke tafiya kan gefen titi da kuma wadada suke kan keke da wata babbar mota a gaban kotun.

Ana tuhumarsa da aikata taadanci bayan da ya hallaka mutum 8 a jiya.

Sayfullo Saipov wanda aka shigo da shi cikin kotun a keken guragu , ana ganin ya samu kwarin gwiwa ne daga kungiyar IS mai ikirarin jihadi

'Yan sanda ne dai suka harbe shi kuma suka raunata shi a wurin da lamarin ya faru a jiya.

Masu bincike sun ce Saipov ya fada mu su yana alfahari da abin da ya aikata.

Hukumar bincike manyan laifuka ta FBI ta ce ta gano mutum na biyu, Muhammadzoir Kadirov , wanda ake yi masa tambayoyi kan rawar da ya taka a harin.