'Pneumonia ya fi ko wanne ciwo kashe kananan yara'

One year-old Hakaroom is treated for severe pneumonia at a health care centre supported by Save the Children in Kapoeta North, South Sudan.

Asalin hoton, Save the Children

Bayanan hoto,

An yi wa wannan yarinya Hakaroom magani a wani asibitin Save the Children bayan da ta kamu da ciwon huhu

Kusan yara miliyan daya ne ke mutuwa a ko wacce shekara daga ciwon huhu, wato Pneumonia, duk da yake maganin da ke warkar da ciwon bai fi naira dari ba, kamar yadda kungiyar Save the Children ta bayyana a ranar Alhamis.

Kungiyar za ta wallafa wani rahoto mai taken 'Fighting for Breath', wato kokawar shakar numfashi, wanda ya zo daidai da kaddamar da gagarumin yaki da ciwon da kungiyar za ta yi a fadin duniya.

Kungiyar kuma na fatan ceto rayuka miliyan daya a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Rahoton ya nuna yadda ciwon ke sanadin kashe yara masu kasa da shekara biyar fiye da duk wani ciwo.

Cutar kan zame sanadin mutuwar yara biyu a cikin wannan rukunin na kananan yara a ko wanne minti daya - kuma wannan adadin ya zarce illar da maleriya da atini da kyanda suke yi idan an hada su gaba dayansu.

Fiye da kashi 80 cikin 100 na yaran da ke mutuwa daga ciwon huhun, yara ne masu shekaru kasa da biyu, wadanda garkuwar jikinsu ta raunata saboda rashin isasshen abinci ko nonon uwa.

Jarirai sun fi fuskantar barazana ga rayukansu a makonnin farko na rayuwarsu.

Kungiyar Save the Children na bukatar da a shirya wani babban taro na shugabannin kasashen duniya domin a sami hobbasa dangane da dakatar da barnar da ciwon huhu ke yi wa yara.

Kungiyar na son a samar da:

  • Magungunan rigakafin ciwon Pneumonia, kuma a kara zuba jari a bangaren samar da kariya daga kamuwa da da cutar;
  • Sai kuma gwamnatoci sun rungumi tsarin yaki da ciwon Pneumonian ta hanyar samar wa ma'aikatan lafiya dabarun gano cutar da warkar da ita cikin sauki da hanzari;
  • Gwamnatoci da masu bada tallafin agaji su tabbatar da ana samar da magunguna ga masu bukata;
  • Tsarin hadin gwuiwa tsakanin gwamnatoci da 'yan kasuwa domin samar da iskar oxygen da zata taimaka wa yaran da suka kamu da cutar.

Maganin Amoxicillin da yaran da suka kamu da cutar ke bukata bai wuce senti talatin na Amurka ba, wato kimanin Naira dari - kuma yana iya ceto ran yaron dake fama da cutar pneumonia a cikin kwana uku zuwa biyar. Amma abin takaici ne cewa babu maganin a kasashen da suka fi fama da wannan cutar kamar Tanzania da Jamhuriyar demokradiyar Kongo.

"Wannan ciwo ne da take maida yara masu kokawar shakar numfashi. Ya kuma saka iyayensu cikin zulumi wanda ya kan koma zaman makoki idan yaran suka mutu", inji Kevin Watkins, shugaban Save the Children UK, wanda shi ne ya jagoranci wallafa rahoton da kungiyar ke fitarwa a yau.

"Bamu da dalilin barin rayukan kananan yara masu yawa suna salwanta a hannun wannan ciwon wanda tuni muke da ilimi da halin kawar da shi".

Asalin hoton, Save the Children

Bayanan hoto,

Hakaroom yarinya mai shekara daya tare da mahaifiyarta bayan ta warke

Hakaroom na daya daga cikin yaran da suka kamu da ciwon na Pneumonia, kuma ciwon ya kusa hallaka ta kafin mahaifiyarta ta kai ta wani asibitin kungiyar Save the Children a Sudan ta Kudu.

Likitoci sun ce da an kara kwana daya ba a kai ta asibitin ba, da Hakaroom ta mutu.

Daga baya an nuna Hakaroom a wani bidiyo tana kokawar shakar numfashi. Amma bayan kwanaki sai aka nuna ta ta sami lafiya, kuma a yanzu tana cikin hayyacinta.

Ta warke daga cutar kuma tuni aka mayar da ita ga iyayenta a wani kauye.

Kungiyar Save the Children na bukatar ganin a yi wa yara masu shekaru kasa da biyu, su miliyan 166 rigakafi kana kuma a dauki matakin taimakawa yara miliyan 400 a fadin duniya a kasashen da basu da ingantattun tsarin kiwon lafiya.

A nahiyar Afirka, kimanin rabin iyaye mata ba sa samun kulawa ta kiwon lafiya a lokutan da suke dauke da juna biyu.

Tsohon babban sakataren MDD, Kofi Annan wanda shi ne shugaban Gidauniyar Kofi Annan Foundation, na goyon bayan wannan yunkurin.

Ya ce kudin maganin rigakafi - na dala 9.15 yayi tsada a kasashen dake fama da talauci:

"Kamfanonin hada magunguna, da gwamnatoci da kuma masu bayar da taimakon agaji har ma da ma'aikatun MDD na da alhakin ganin sun hada kai domin samar da maganin rigakafi mai arha domin a kara ceto rayuka masu yawa".