Mukarraban Buhari sun yi cacar baki a fadar gwamnati

. Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Wasu na ganin wannan abu da ya faru ba abin mamaki ba ne a gwamnatin Buhari

'Yan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta da muhawara kan cacar bakin da ta faru tsakanin wasu manyan jami'an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A ranar Laraba ne Shugaban Mai'aikatan fadar gwamnatin Najeriya Abba Kyari, da shugabar ma'aikatan tarayyar kasar Winifred Ita-Oyo, suka yi cacar baki a fadar gwamnati shugaban kasar jim kadan kafin fara taron majalisar zartarwa.

Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna Abba Kyari da Winifred Ita-Oyo, suna cacar baki a gaban mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da mai bai wa shugaban kasar shawara kan al'amuran tsaro, Babagana Monguno.

Ko da yake babu tabbacin abin da mukarraban gwamnatin suke fada a cikin hoton bidiyon, sai dai wasu kafofin yada labaran kasar sun ba da rahoton cewar sun yi ce-ce-ku-cen ne kan batun mayar da tsohon shugaban kwamitin garambawul ga tsarin fanshon Najeriya, Abdulrasheed Maina.

Bayan ta bayyana cewa an mayar da Abdulrasheed Maina wanda hukumar EFCC ke nema ruwa-a-jallo bakin aikin gwamnati, Shugaba Buhari ya nemi Mrs Ita-Oyo, ta rubuta yadda aka yi Abdulrasheed ya koma bakin aiki da kuma wadanda ke da hannu a lamarin kuma ta mika takardar ga Abba Kyari.

Bayan haka ne jaridu suka ruwaito cewar an kwarmata bayanan da ke cikin takardar da Winifred Ita-Oyo ta mika wa shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Abba Kyari.

A cewar jaridun Najeriyar, kwarmata bayanan cikin wannan takardar ce silar cacar bakin da mukarraban gwamnatin biyu suka yi.

Hakkin mallakar hoto Youtube Channels TV

Mafi yawan masu sharhi a shafin Twitter sun yi tur da wannan al'amari da ya faru tsakanin manyan jami'an gwamnati biyu, inda wasu ke cewa ba su yi mamakin faruwar hakan ba a gwamnatin Buharin, "wacce ke cike da rudani."

Sai dai mafi yawan wadanda suka yi tsokaci ba su nuna goyon bayansu ga ko wanne daya daga cikin jami'an da suka yi cacar bakin ba.

Wani Ibrahim Musa Aliyu ya rubuta cewa: "Abba kyari, na daya daga cikin matsalolin gwamnatin nan. Amma Buhari ya kasa ganewa, shi yake tafiyar da kusan komai."

"Haka za a ci gaba da wannan wasan kwaikwayon in har ba a yi abin da ya dace ba a wannan gwamnatin," kamar yadda Alagba Ken ya bayyana a Twitter.

Wannan ce-ce-ku-cen ya bayyana ne bayan da a baya-bayan nan gwamnatin Shugaba Buhari ta samu yabo daga wasu magoya bayanta kan korar tsohon sakataren gwamnatin tarayyara kasar, Babachir David Lawal, da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar, Ayodele Oke.