Yadda wata jibgegiyar kada ta shiga gidan wani mutum

The 3m (12ft) long crocodile

Asalin hoton, Kishore Dash

Bayanan hoto,

Mutanen kauyen sun taru suka kama kadar kuma suka daure ta a jikin bishiya

Wani mutum a wani kauye a jihar Orissa na gabashin Indiya ya wayi gari da wani bako mai ban tsoro a gidansa - inda ya ci karo da wata jibgegiyar kada mai tsayin mita 4 (12ft).

Dasharath Madkami ya ce ya ga kadar ne lokacin da wata kara ta tashe shi karfe 03:00 na dare.

Ya ce nan da nan sai ya ankarar da sauran mutanen kauyen wadanda suka taru suka kama kadar kuma suka daure ta a jikin bishiya.

Da farko dai mutanen kauyen sun so su kashe kadar ne, amma sai dagacinsu ya hana su.

Daga baya hukumomin kula da namun daji na yankin sun je sun karbi kadar.

Asalin hoton, Kishore Dash

Bayanan hoto,

An samu sabanin ra'ayi game da sakin kadar

An samu sabanin ra'ayi game da sakin kadar.

Jami'an namun daji sun so su mayar da ita wata madatsar ruwa ta Satiguda, inda ta fito, amma mazauna kauyen suka ki don tsoron cewa za ta iya koma wa kauyen.

Wani jami'in daji Sushant Nayak ya fada wa BBC cewa: "Akwai kada kusan 30-40 a madatsar ruwa ta Satiguda."

YA kara da cewa: "Ana zaton cewa wannan kadar ta samu fitowa ne daga dam din ta shiga kauyen wanda ba shi da nisa da wajen don saka kwai."

An saki kadar ne cikin matattarar ruwa ta Balimela, mai nisan kilomita 37.