Mummunan yanayi ya sa mutum miliyan 200 barin gidajensu

Mummunan yanayi

Asalin hoton, Getty Images

Mummunan yanayi ya tursasawa kusan mutane miliyan 200 a sassan duniya gudun hijira a cikin shekara tara da suka gabata, kamar yadda wani rahoton kungiyar Oxfam da ke ba da tallafin abinci ya bayyana.

Rahoton ya ce matsalar ta fi shafar kasashe masu fama da talauci inda sama da mutane miliyan uku suka yi kaura a wannan shekarar kawai, kusan kashi biyu bisa uku kenan.

Bisa ga wadannan alkaluma, rahoton ya ce mutane daga kasashe masu karamin karfi da matsakaita za su fi fuskantar matsalar da kusan kashi biyar, fiye da mutanen da ke kasashe masu arziki.

Rahoton ya ce adadin yawan mutanen da za su kauracewa gidajensu zai karu idan aka samu karuwar tumbatsar teku da kwararowar hamada.

Rahoton na Oxfam ya yi la'akari ne da matsaloli na mahaukaciyar guguwa da ake fuskanta a kasashen Caribbean da Pacific, da fari a Afirka da Asiya da sauran bala'o'i da ake fuskanta na yau da kullum.

Jami'in Oxfam da ya rubuta rahoton Simon Bradshow, ya shaidawa BBC cewa kaura da ake yi babbar matsala ce domin har yanzu duniya ta gaza tantance adadin yawan 'yan gudun hijira da matsalar sauyin yanayi ya tursasawa kauracewa gidajensu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rahoton ya yi la'akari ne da matsaloli na mahaukaciyar guguwa a kasashen Caribbean da fari a Afirka da Asiya

Masana kimiya sun ce sauyin yanayi na kara tsananta mumunan yanayin da ake fuskanta a duniya, kuma talakawa ne abin ya fi yi wa illa.

Sannan masanan sun yi gargadi kan cewa nan da dan lokaci ruwa zai shafe gonaki da gidajen talakawa.

Ana sa ran taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi da za a gudanar a birnin Bonn na Jamus a makon gobe, zai tattauna wannan matsalar gudun hijira da mutane ke yi sakamakon mummunan yanayi da kuma hanyoyin tunkarar matsalar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sannan masanan sun yi gargadi kan cewa nan da dan lokaci ruwa zai shafe gonaki da gidajen talakawa