An kama motocin alfarma 51 a wani gida a Lagos

An kama manyan motoci 51 a wani gida a Lagos

Hukumar yaki da fasa kwauri mai kula da shiyyar kudu maso yammacin Najeriya ta kama manyan motoci 51 a wani gida da ke a unguwar Ikoyi a birnin Legas.

Kontirola na kostom mai kula da shiyyar, Muhammad Uba Garba ne ya bayyana hakan ga wakilin BBC, Umar Shehu Elleman a Legas.

Ya ce kudin manyan motocin 51 sun kama a kan naira 1.76bn, biliyan daya da miyan saba'in da shida.

Motocin dai an kama su a lokaci daya a kuma gida daya a sakamakon bayanan sirri da suka tabbatar da shigo da motocin ta barauniyar hanya.

Motocin dai duk kirar bana ne na shekara ta 2017. A cikin motocin akwai kirar Prado Jeep da Land Cruiser Jeep da Lexus Jeep da danginsu.

A cewar shugaban hukumar ta kostom ko wacce daya ta kan kama daga naira miliyan 40 zuwa miliyan 70 a kasuwa.

Yanzu haka dai an kama mutum biyu, kuma jami'an hukumar na ci gaba da tatsar bayanai domin gano ko su wane ne masu motocin.

Hukumar dai ta ce a cikin motocin 50 akwai hudu wadanda masu sulke ne, wadanda kafin a shigo da su a an samu amincewar babban jami'i mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.

To ko doka ta bai wa hukumar kwastam umarnin shigowa cikin gari da gidajen mutane domin gudanar da bincike da kuma kayayyakin da ake zargi na fasa kwauri ne?

Kontirola Uba ya ce akwai wani bangare na doka sashi na 147 da ya ba su izinin shiga gidaje muddun aka samu tabbacin akwai kayayyaki da aka hana shigo da su Najeriya ba bisa ka'ida ba ko kuma ba a biya musu haraji ba.

Hukumar ta ce bayan kwana 30 wadannan motoci za su zama mallakar gwamnatin tarayya.