Kyauren jirgin sama ya fado a kan wani gida

The door weighed more than 20kgs

Asalin hoton, Telangana Police

Bayanan hoto,

Nauyin kofar jirgin ya kai kilo 20

Iyalan wani gida a Indiya sun shiga halin firgici a yayin da kofar wani jirgin sama ta fado a kan rufin gidansu a birnin Hyderabad.

Allah ya taimaki wani mutum da ke yi wa rufin kwanon gidan fenti ya tsira, don ya tafi cin abinci a lokacin da al'amarin ya faru.

Wani jami'in 'yan sanda ya shaida wa sashen BBC Telugu cewa al'amarin ya faru ne a yayin da karamin jirgin mai daukar mutum hudu ke tafiya kasa-kasa a sararin samaniya.

Ya kara da cewa matukin jirgin da wanda yake koya wa ma sun tsira, kuma tuni aka kaddamar da bincike don sanin ainihin abun da ya jawo faruwar lamarin.

Wani sufeton 'yan sanda Karan Kumar Singh, ya ce: "abu ne da aka saba gani jirgin koyon tuki na yawo kasa-kasa a sararin samaniya a wannan yankin."

A watan Satumba ma wani matukin jirgi da wanda yake koyawa sun sha da kyar inda suka tsira da jin raunuka a irin wannan al'amari, inda jirgin da suke ciki ya fadi a yankin na Hyderabad.