Gurbataccen abinci ya yi wa dalibai illa a Ghana

Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Wasu daliban wata babbar makarantar sakandire a Ghana, Senior High School (GHANASS) sama da hamsin ne suka shiga wani yanayi, bayan cin wani abinci da ya gurbace.

Daliban sun fara korafin ciwon ciki ne bayan sun ci wake a kantin da ake sayar da abinci na makarantar da ke garin Kofridua a karshen mako.

Ba tare da bata lokaci ba ne aka garzaya da daliban asibitin St Joseph da ke garin don ba su taimakon gaggawa, inda ae ba su kulawa ta musamman.

Wakilin BBC da ke Ghana ya ce a lokacin da manema labari suka kai ziyara asibitin sun tarar ana karawa wasu daga cikin daliban ruwa.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron rahoton Muhammad Fahad Adam a kan wannan labari:

Bayanan sauti

Rahoton Fahad kan dalibai a Ghana