EFCC na binciken Ayo Oke kan kudin da aka samu a legas

Ofishin EFCC dake Legas Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta gayyaci tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasar, Ambasada Ayodele Oke da mai dakinsa domin amsa wasu tambayoyi dangane da kudi dala miliyan 43 da aka samu a wani gida a Legas.

Bayanan da BBC ta samu daga hukumar ta EFCC dai sun nuna cewa hukumar ta bukaci Mista Oke da matarsa su kai kansu a ofishinta na yanki dake Legas.

Wannan ya biyo bayan korar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi wa Mista Oke daga aiki bayan da wani rahoto ya same shi da hannu a almundahana.

Wani babban jami'i a hukumar ta EFCC ya shaida wa BBC cewa suna neman karin bayani ne daga Mista Oke da mai dakinsa game da wadannan makudan kudin da aka samu a wani gida dake karkashin hukumar da ya shugabanta.

Sauran wadanda hukumar ta gayyata domin su amsa tambayoyi game da kudaden sun hada da wani mai hada-hadar canjin kudi, da wani kamfanin hada-hadar man fetur da gas da kuma wasu jami'an hukumar ta tattara bayanan siri, wato NIA.

Tun a watan Afrilu ne dai hukumar ta gayyaci mai dakin Mista Oke amma sai ba ta je ba saboda kwamitin shugaba Muhammadu Buhari ya kafa a wancan lokacin don ya binciki lamarin.

Sai bayan kwanaki biyu da shugaba Buhari ya sanar da korarsa daga aiki, tare da sakataren gwamnatin kasar ne hukumar ta EFCC ta sake ci gaba da binciken lamarin, bayan da fadar shugaban ta umarce ta da ta ci gaba da yin hakan.

Akwai alamun cewa hukumar ta EFCC ta samu kofen rahoton kwamitin da ya binciki badakalar wanda mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya jagoranta kuma tuni ya mika wa shugaban kasar.

Haka ma wasu bayanan suna nuna cewa mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu ne da kansa ke jagorantar wannan binciken.

A watan Yunin da ya gabata ne wata kotun tarayya a Legas ta bai wa gwamnati damar karba da kuma amfani da kudin tun da babu wanda ya bayyana a gaban kotun cewa kudin nasa ne.