Egypt: An daure matar da ce mata na iya haihuwa babu aure

Doaa Salah ta sanya kayan mata masu ciki a yayin da take gabatar da shirin talabijin Hakkin mallakar hoto Al Nahar TV
Image caption Doaa Salah ta sanya kayan mata masu ciki a yayin da take gabatar da shirin talabijin wanda ya janyo cece-kuce a Masar

Wata kotu a Masar ta daure wata mai gabatar da wani shirin talabijin tsawon shekara uku a kurkuku domin ta tattauna hanyoyin da mata kan iya daukar ciki ba tare da sun yi aure ba.

Doaa Salah wacce mai gabatar da shirin talabijin ne a tashar Al-Nahar TV, ta tambayi masu kallon shirinta ko sun taba tunanin saduwa da wani ko wata kafin aure.

Ta kuma basu shawarar cewa mace na iya yin aure na wani takaitaccen lokaci domin ta sami 'ya'ya kana sai ta kashe auren nata domin tayi zamanta tare da 'ya'yanta.

An tuhume ta da keta mutumcin al'adun kasar, kuma an yanke mata hukunci.

Kotun kuma ta umarce ta da ta biya kudin diyya na fam 10,000 na kudin Masar (fam 430 na Ingila).

Hukumomi sun ce shawarwarin da ta watsa a cikin shirin nata "sun keta haddin rayuwar mutanen Masar", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na EFE ya ruwaito.

Doaa Salah, wacce ba matar aure bace ita kanta, ta shawarci mata cewa suna iya biyan wani ya aure su na dan wani lokaci, kuma tayi bayanin yadda a kasashen waje maza ke bayar da maniyinsu kyauta domin mata masu bukatar haihuwa - amma ta ce wannan halayyar bata samu karbuwa ba a Masar.

A yayin da take gabatar da shirin nata da ya janyo kace-nace, ta fada wa masu kallo cewa: "Idan kika kashe aurenki, zaki kasance uwa maras miji. Kuma idan mijinki ya mutu, shi ma zaki zama uwa maras miji. Watakila ya kamata ki sani cewa kina da zabin zama uwa maras miji ba sai kin yi aure ba, ko?"

Ta kuma ce ana tattauna batun ne saboda, "bukatar haihuwa da samun 'ya'ya, lamarin da maza basa iya fahimta".

Tashar talabijin ta Al-Nahar ta dakatar da ita na tsawon wata uku bayan da ta gabatar da wannan shirin, gabanin a gurfanar da ita a gaban shari'a.

Matar na iya daukaka kara akan wannan hukuncin na daurin shekara uku da aka yanke mata.

Labarai masu alaka