Nigeria: Hukumar EFCC ta fara binciken Babachir

  • Abdulwasiu Hassan
  • BBC Hausa, Abuja
Getty

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A farkon makon nan ne aka kori Mista Babachir

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta fara binciken tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal.

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC cewa hukumar ta fara binkar tsohon sakataren gwamnatin kasar.

Hakazalika rahotanni sun ce hukumar ta hada wasu jami'ai masu bincike na musamman domin bincikar kwangilar yanke ciwaya ta naira miliyan 200 da aka alakanta ta da Babachir.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya dakatar Babachir da kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin Najeriya, Ayo Oke, daga bakin aiki ne a watan Afrilun 2017.

San nan ya kafa wani kwamitin bincike domin ya binciki zarge-zargen da aka yi musu na aikata ba daidai ba.

Shugaban dai ya bai wa kwamitin da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta wa'adin kwana 14 a matsayin lokacin da zai ba shi rahoton bincikensa.

Sai dai kwamitin bai samu ya mika mishi sakamakon binciken a kan lokaci ba domin shugaban ya tafi jinya kasar Birtaniya.

Da shugaban ya dawo daga Landan a watan Agusta, bai dauki mataki akan rahoton kwamitin ba, lamarin da ya jayo wa gwamnatinsa suka.

Ranar 30 ga watan Oktoba ne shugaban ya kori Babachir Lawal da Ayo Oke daga aiki, matakin da masu suka suka ce bai wadatar ba.

Masu sukan sun bukaci gwamnatin ta gurfanar da mutanen a gaban kotu, inda wasunsu suka yi zargin cewa Shugaba Buhari ba ya so a hukunta makusantar shi idan suka yi laifi.

Sai dai mai taimaka wa Shugaba Buhari na musamman kan watsa labarai, Garba Shehu, ya musanta zargin yana mai cewa shugaban ba ya saka baki a aikin hukumomin kasar.

Labarin binciken da EFCC take yi wa Babachir na zuwa ne a lokacin da hukumar ta fara bincikar tsohon shugaban hukumar leken asirin Najeriya, Ayo Oke, da matarsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya kori ambasada Ayo Oke ne da shugaban hukumar