Mata ba za su yi daidai da maza ba nan da shekara 100 – WEF

Girls in Yemen classroom take an exam in image taken in 2016 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahoton ya yi nazari kan kasashe 144 a fannin tattalin arziki da ilimi da siyasa da kuma kiwon lafiya

Wata kungiya mai sa ido kan tattalin arziki ta ce za a dauki kusan shekara 100 kafin a cike gibin batun daidaito tsakanin maza da mata a duniya.

Wannan ne karo na farko da bayanai daga Taron Tattalin Arziƙi na Duniya (WEF) ya nuna cewa kusan duk shekara sai an samu wawagegen gibi a batun daidatin jinsi, tun bayan da ta fara tattara bayanai kan hakan.

Rahoton ya yi nazari kan kasashe 144 a fannin tattalin arziki da ilimi da siyasa da kuma kiwon lafiya.

An gano cewa kashi 68% na mata sun fi samun damarmaki fiye da maza.

Wannan ya ragu daga kashi 68.3% bisa 100 a bara.

Taron ya ce za a dauki shekara 100 kafin a samu daidaton jinsi a duniya, ba kamar yadda aka yi hasashen cewa za a dauki shekkara 83 ba a shekarar 2016.

An fi samun daidaiton jinsi a al'amuran kiwon lafiya da ilimi, in ji shi, amma akwai wawagegen gibi a bangarorin tattalin arziki da kuma siyasa.

Mata za su jira har nan da shekaru 217 kafin su samu yawan abun da maza ke samu a wuraren aiki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasashen yankin Nordic sune inda aka fi samun daidaton jinsi. Iceland a sama a jerinsu da kashi 12 cikin 100, yayin da Norway da Finland da kuma Sweden suke bin bayanta.

Rwanda ce ta hudu a cikin jerin kasashen da aka fi samun don daidaito tsakanin jinsi da 18%.

Kasar tana da yawan mata a majalisar dokoki a duniya - ana samun mata uku a ciki duk mutum biyar.

Nicaragua da Slovenia da Ireland da New Zealand da kuma Filipins ma na cikin jerin kasashe 10.

Mata a Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka sune wadanda suka fi fuskantar matsalar daidaiton jinsi.

Rahoton ya ceidan aka cike gibin tattalin arziki:

  • China za ta kara samun $2.5tn a ma'aunin tattalin arzikinta
  • Amurka za ta iya ƙara samun $1,750bn
  • Faransa da Jamus za su iya kara fiye da dala 300bn ko wannensu
  • Birtaniya za ta iya ƙara $ 250bn
Hakkin mallakar hoto White House
Image caption Mata a Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka sune wadanda suka fi fuskantar matsalar daidaiton jinsi

Labarai masu alaka

Karin bayani