Abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

Zababbun hotuna masu kayatarwa daga sassa daban-daban na Afirka da aka dauka a makon jiya.

Siyum Haile, 72, a retired United Nations (UN) employee and Jehovah's Witness, poses for a photograph next to his 1977 model Volkswagen Beetle car in Addis Ababa, Ethiopia - 16 September 2017 - photo published 27 October 2017

Asalin hoton, Reuters

Wata mota kirar Beetle ta ainahi na iya zama wani abu mai ban sha'awa a wasu wurare a kwanakin nan, amma ban da Habasha ba. A wannan hoton da kamfanin dillanci labarai Reuters ya wallafa a ranar Juma'a, wani mutum ne ya harde a kan motarsa samfurin shekarar 1977, yana yabon motar da karkonta da rashin tsadarta.

Asalin hoton, Reuters

Wani lokaci, kawai kana bukatar dan taimako kadan ne. Wannan yaron yana addu'a don fara jarrabawar firamare, wanda za a yi makarantar firamare ta Kiboro a Nairobi babban birnin Kenya ranar Talata.

Asalin hoton, AFP

A wani waje a kasar Kenya kuwa, sake gudanar da zabe na jan hankalin jama'a. A ranar Litinin, wadannan mutane sun mayar da hankali ne kan abubuwan da ake nunawa a talabijin a wani shagon sayar da kayan lantarki a Kisumu.

Asalin hoton, AFP

Wani mai taswira yana zana hoton zanen barkwanci na kasr Japan, yayin wani taron nishadantarwa a babban birnin Libya, Tripoli, ranar Alhamis. An fara gudanar da irin wannan gagarumin taron masu goyon bayan zanen barkwancin ne a San Diego a shekarun 1970.

Asalin hoton, AFP

A Masar kuwa, dubban mutane sun hadu don kallon wasan karshe na kungiyar Ahly ta Alkahira kafin su tafi wasa Moroko a gasar zakarun nahiyar Afirka ta karshe.

Abin bakin ciki ga wadannan magoya bayan shi ne daga wasan da ka yi saboda yawan 'yan kallo.

Asalin hoton, EPA

A Ivory Coast, wata mace tana tace manja a gargajiyence, a ranar Litinin.

Ana amfani da manja ta hanyoyi ya dama, ana iya amfani da shi wajen hada sabulu zuwa makamashi da aka samo daga tsirrai, kuma gwamnatin kasar Ivory Coast na fatan samar da kayayyakin amfani zuwa ton dubu 600 nan da shekarar 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Wadannan masu gasar a Libya duk sun zabi su shafe yinin ranar Asabar don kammala wani matakin wasa na tsawon kilomita hudu - ciki kuwa har da rarrafe a karkashin wani shinge.

Asalin hoton, Google

Wadannan matuka jirgin ruwan suna tafiy ne a zagaye na uku na zagaye duniya da suke yi a teku. Sun tashi cikin shiri sosai daga kasar Cape Town a ranar Talata don ci gaba da tafiya da kuma yiwuwar haduwa da iska mai karfi.

Asalin hoton, AFP

Wadannan yaran wasa ne cikin baraguzan wani gini da ya rushe a yankin Kasai da ke tsakiyar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inda suke nishadantar da kansu a wannan yanki da ke fama da tashin hankali a cikin 'yan shekarun nan.

Asalin hoton, PA

A karshe kuma wanan hoton 'yan wasan Rwanda ne a lokacin da suke wasan kurket. Tsohon kyaftin din Ingila Michael Vaughan da kuma tsohon dan kwallon Afrika ta Kudu Herschelle Gibbs ne suka jagoranci gasar a ranar Asabar a sabon filin wasa na Kigali.

Hotuna daga AFP da EPA da PA da kuma Reuters